Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta Kudu ta dakatar da ayyukan jakadanci a Nijeriya
2019-09-06 10:46:47        cri

Wakilin kasar Afrika ta Kudu, Bobby Monroe, ya tabbatar da rufe ofisoshin jakadanci kasar dake kasar Nijeriya, matakin da ya dakatar da duk wani aikin jakadanci a kasar dake yammacin Afrika.

Bobby Monroe ya ce, an dauki matakin ne domin fargabar ramuwar gayya game da harin kin jinin baki da ake kai wa 'yan Nijeriya a Afrika ta Kudu, inda ya tabbatar da cewa, sun rufe ofisoshinsu dake Abuja da Lagos, har zuwa lokacin da lamura za su dawo daidai.

Bobby Monroe ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) cewa, an rufe ofisoshin ne bisa umarnin gwamnatin kasar ta Afrika ta Kudu.

Sai dai, Ministan harkokin wajen Nijeriya, Geoffrey Onyeama, ya shaidawa kamfanin dallancin labarai na Xinhua cewa, Afrika ta Kudu ba ta sanar da hukumomin Nijeriya matakin nata a hukumance ba tukuna.

'Yan sandan Nijeriya dai, sun kara kaimi wajen yin sintiri yayin da ake tsaka da zanga-zangar adawa da hare-haren kin jinin baki a Afrika ta Kudu a wasu sassan kasar, inda suka lashi takobin kare jami'an diflomasiyya da ofisoshin jakadanci.

Cikin wata sanar da aka fitar jiya, Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya ce ya ba da umarnin tsaurara tsaro a wuraren da ofisoshin jakadanci da baki da harkokin kasuwancinsu suke. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China