Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sudan ya sanar da kafa majalisar ministocin gwamnatin wucin gadi
2019-09-06 09:38:34        cri

Firaministan kasar Sudan Abdalla Hamdok, ya sanar da kafa majalisar ministoci ta gwamnatin wucin gadi, karo na farko, tun bayan hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

Abdalla Hamdok, ya ba da sanarwar ne a jiya, yayin wani taron manema labarai a Khartoum, yana mai dogaro da dokar kundin tsarin mulki da shugaban gwamnatin wucin gadi na kasar ya gabatar.

Dokar ta nada ministoci 18, sai dai an jinkirta nada ministoci 2 na ma'aikatun kula da ababen more rayuwa da sufuri da kuma na kula da dabbobin gida da kiwon kifi.

Karkashin dokar, an nada Jamal Omer a matsayin ministan tsaro da Al-Teraifi Idriss, matsayin minitsan harkokin cikin gida. Wadannan ministoci 2, su ne wadanda bangaren soji na gwamnatin kasar ya nada.

Ministocin 18 sun hada da mata 4, kuma daga cikinsu aka samu mace ta farko da ta kasance ministar harkokin wajen kasar wato, Asma Mohammed Abdullah.

Firaministan ya kuma jaddada cewa, abubuwa mafiya muhimmanci da sabuwar gwamnatin kasar take son cimmawa su ne, wanzar da zaman lafiya da kawo karshen yaki da kuma aiwatar da gyare-gyare ga tsarin tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China