Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Libya dake gabashin kasar sun kaddamar da hari ta jiragen sama a kusa da birnin Gharyan
2019-09-01 16:24:59        cri
A jiya Asabar sojojin saman kasar Libya dake da sansani a gabashin kasar sun kaddamar da hare hare ta jiragen sama a yankin dakarun gwamnatin kasar masu samun goyon bayan MDD a kusa da birnin Gharyan, mai tazarar kilomita 80 daga babban birnin kasar Tripoli.

Sojojin sun yi kokarin kaddamar da hari kan dakarun gwamnatin a sansaninsu dake birnin Gharyan, inda suka hallaka sojojin gwamnati biyu, kana suka lalata motocin sojojin masu yawa, cibiyar sojojin dake gabashin kasar ne ta sanar da hakan.

Kawo yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin mai samun goyon bayan MDD game da harin.

Kwanaki kadan da suka gabata, gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD ta sanar cewa, ta yi nasarar dakile wani harin da dakarun sojojin gabashin kasar suka shirya kaiwa a kusa da birnin Gharyan.

Daga bisani a watan jiya, dakarun gwamnatin Libyan sun sanar da karbe ikon birnin Gharyan inda suka fatattaki sojojin dake da sansani a gabashin kasar.

Gwamantin Libyan mai samun goyon bayan MDD ta jima tana gwabza yaki da sojojin gwamnati mai sansani a gabashin kasar tun daga farkon watan Afrilu, a yankunan Tripoli da kewayensa, domin neman kawar da dakarun sojojin masu sansani a gabashin kasar, wadanda ke cigaba da fafatawa da nufin kwace ikon babban birnin kana da yunkurin kifar da gwamnatin Libyan mai samun goyon bayan MDDr. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China