Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana ci gaba da ba da gudunmawarta wajen dunkulewar tattalin arzikin duniya na bai daya
2019-08-27 16:05:14        cri
Gidan radiyon kasar Sin CRI ya ba da bayani a yau mai taken "Habaka yankin ciniki cikin 'yanci: Sin tana ci gaba da ba da gudunmawarta wajen dunkulewar tattalin arzikin duniya na bai daya".

Bayani ya nuna cewa, jiya Litinin Sin ta gabatar da jerin sabbin sunayen yankin gwaji na yin ciniki cikin 'yanci ciki har da lardunan Shandong, Jiangsu, Guangxi, Hebei, Yunnan da Heilongjiang, hakan ya sa adadin irin wadannan yankuna ya karu zuwa 18 a kasar. Ana iya ganin cewa, duk da cewar Amurka ta tada takaddamar ciniki tsakaninta da kasar Sin a cikin shekara daya da wani abu da suka gabata, amma Sin tana nacewa ga tsarin da ta tsayar, wato habaka bude kofa ga kasashen waje, matakin da ya sa, Sin ta ci gaba da ba da gudunmawarta wajen dunkulewar tattalin arzikin duniya na bai daya da kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai bude kofa.

Bayanin ya jaddada cewa, Sin ta rika daga matsayinta na bude kofa ga ketare, matakin da ya baiwa duk duniya sabbin damammaki wajen samun bunkasuwa. A yayin da wasu kasashe na ci gaba da daukar manufar kariyar cinikayya a halin yanzu, Sin ta nace ga manufar kara bude kofa, matakin da ya bayyanawa duk duniya cewa, Sin ta goyi bayan dunkulewar tattalin arzikin duniya na bai daya da maraba da kamfanonin ketare su zuba jari a kasar, tare kuma da samar da dammamakin samun bunkasuwa a kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China