Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin wallafa na zamani na kasar Sin ya samu fiye da yuan biliyan 800 a kudin shigarsa na shekara
2019-08-26 14:41:32        cri
Rahotanni sun nuna cewa kudaden shiga na shekara-shekara na kamfanin wallafa na zamani na cikin gidan kasar Sin a shekarar 2018 ya kai yuan biliyan 833.078, inda ya karu da kashi 17.8% idan an kwatanta da shekarar da ta gabata. Rahoton, mai taken "Rahoton shekara na kamfanin wallafa na zamani na shekarar 2018-2019", wanda aka bayyana a babban taron kolin dandalin hukumar wallafa ta zamani ta kasar Sin, da aka gudanar kwanan nan a birnin Beijing.

Rahoton ya bayyana cewa, wallafar da ake yi ta wayoyin hannu da wasanni ta shafukan intanet sun kasance muhimman ginshikai na samun kudaden shigar kamfanin wallafa na zamani. Fasahar 5G za ta samar da karin ingantaccen yanayi ga sabbin manhajoji na fasahar zamani, da kafofin sadarwa na zamani, da sabon tsari a fannin wallafa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China