Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Eritrea ta yaba da tallafin tawagar kiwon lafiyar kasar Sin
2019-08-26 10:42:33        cri
Ma'aikatar yada labarai ta kasar Eritrea ta ce gwamnatin kasar ta gabashin Afrika ta yaba da tallafin kiwon lafiya wanda tawagar ba da agajin kiwon lafiya ta kasar Sin take gudanarwa a kasar. A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ma'aikatar yada labaran kasar ta yaba aikin da tawagar tallafin kiwon lafiyar ta kasar Sin ta gudanar a kasar wanda ta kammala wa'adin aikinta na tsawon shekara guda.

Sanarwar ta kara da cewa, aikin da tawagar tallafin kiwon lafiyar ta kasar Sin ta gudanar a kasar Eritrea ya kara bayyana kakkarfar dangantakar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu.

Tawagar kiwon lafiyar ta kasar Sin, ta kunshi likitoci, wadanda suka samar da aikin jiyya kyauta ga jama'ar kasar Eritrea a tsawon shekara guda, sun kammala aikinsu a ranar Asabar. Kwararrun likitocin Sinawa sun gudanar da ayyukan kiwon lafiya ne a asibitoci daban daban a kasar Eritrea.

A cewar ofishin jakadancin kasar Sin a Eritrea, sama da likitoci sinawa da sauran kwararrun jami'an kiwon 200 ne suka gudanar da aikin jiyya kyauta a kasar Eritrea tun daga shekarar 1997. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China