Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rawar da kasar Sin ke takawa wajen kyautata muhalli ta hanyar sarrafa bola
2019-08-23 10:15:47        cri

Wata kididdigar da hukumar dake da alhakin kula da tarkaken bola da ake shigarwa kasar Sin ta fitar kwanan nan ya nuna cewa, yawan bolar da ake shigarwa kasar ya ragu da kashi 30 bisa 100 a cikin watanni shidan farkon wannan shekarar idan an kwatanta da makamancin lokacin bara. A halin yanzu adadin ya kasance ton biliyan 7.2 wanda ya ragu da kashi 28.1% a makamancin lokacin bara, hakan yana kara bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen inganta shirin hana shigar da tarkacen bola kasar daga kasashen ketare ba bisa ka'ida ba.

Gabanin shekarar 2017, kasar ta kasance tamkar wani wajen jibge shara mafi girma a duniya. Wata kididdigar MDD ta nuna cewa, kasar Sin ita ce ke karbar kusan rabin tarkacen bolar da ake samarwar a duniya baki daya tun daga shekarar 1992. Manyan hanyoyin hudu dake samar da tilin bolar sun hada da Amurka, nahiyar Turai, da Japan, da Australiya. Kididdigar ta nuna cewa, matsalolin gurbatar muhallin da kasar Sin ke fuskanta cikin shekaru 20 da suka gabata ya samo asali ne sakamakon yawan bolar da kasar Sin ke sarrafawa wanda yakai kashi 50% na adadin yawan bolar duniya baki daya.

Bisa la'akari da alkaluman kididigar da bangarori daban daban dake shafar muhalli na duniya suka gabatar ciki har da hukumomin MDD, hakan ya nuna cewa gwamnatin kasar Sin da manyan kamfanonin dake sarrafa shara na kasar Sin, har ma da irin manyan fasahohin da Sin ke amfani da su wajen gudanar da wannan gagarumin aiki za'a iya cewa ba kawai sun taimakawa kasar Sin ba ne, har ma sun taimakawa kasa da kasa wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu na kula da kuma sarrafa tarin bola wacce ke zama a matsayin babbar barazanar dake haifar da gurbata muhallin da dan adam ke rayuwa cikinsa a duniya. Ko shaka babu, mataki da gwamnatin kasar Sin ta dauka na tsara dokokin da za su kawo sauye sauye game da batun shigo da tarkecen bola daga kasashen waje zuwa cikin kasar ba zai taba zama aibu ba, dalili kuwa shi ne, ba zai taba yiwuwa kasar ta zama tamkar abin da masu hikimar magana ke cewa kura da shan bugu gardi da kwashe kudi ba, misali kididdigar da MDD ta fitar dake nuna cewa wasu manyan kasashen yammacin duniya suna daga cikin kasashen dake sahun gaba wajen shigar da tilin shara zuwa kasar Sin amma suna fakewa wajen sukarta da wasu zarge zarge masara tushe balle makama, duk da irin rawar da kasar ke takawa wajen raya ci gaban tattalin arzikin duniya, musamman wajen shirin yaki da fatara, da yadda take jan kasashe masu tasowa jikinta musamman kasashen Afrika wajen kulla dangantaka da mu'amala wacce kowane bangare ke cin gajiya, dadin dadawa, bisa irin rawar da kasar ke takawa wajen samar da ayyukan gina ababen more rayuwar jama'a, da kuma irin tallafin da gwamnatin Sin ke bayarwa wajen aikin wanzar da zaman lafiya da jinkai bil adama a kasashen daban daban na duniya, alal hakika bai dace wasu kasashen yammacin duniya su dinga fakewa da guzuma suna harbin karsana ba, ai idan har amarya ba ta hau doki ba to bai kamata a aza mata kaya ba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China