Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Kasashen Afirka za su iya cin gajiyar matakan bude kofa da inganta muhallin zuba jari da kasar Sin take dauka
2019-08-23 10:13:13        cri

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana aniyar mahukuntan kasar na daukar matakan da suka wajaba, don ganin an samar da damammaki na zuba jari daga waje, da gina kyakkyawan yanayi, wanda zai ba da damar takara a mataki na kasa da kasa.

Da yake tabbatar da hakan yayin wani taron karawa juna sani a jiya Laraba, mataimakin minista a ma'aikatar cinikayyar kasar Qian Keming, ya ce Sin za ta ci gaba da samar da damammakin zuba jari ga kamfanoni na kasa da kasa, da zakulo hanyoyin inganta muhallin zuba jari, cikin adalci, kuma a bude, wanda kuma za a iya fahimtar yanayin sa. Qian ya ce kamfanonin kasa da kasa muhimman abokan hulda ne, dake ganin halin da ake ciki a Sin, suna kuma ba da gudummawa, tare da cin gajiya daga manufofin Sin na gudanar da gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje cikin shekaru 40 da suka gabata.

Wasu alkaluman ma'aikatar cinikayyar Sin sun nuna cewa, kawo yanzu kimanin manyan kamfanoni 490, cikin kamfanoni mafiya girma 500 dake sassan duniya ne suka zuba jari a kasar Sin.

Karkashin wannan manufa, tuni kasar Sin ta gabatarwa sassan duniya shawarar "Ziri daya da hanya daya" wadda ta tanaji shiga hadin gwiwa, ta samar da ababen more rayuwa, da cudanyar cinikayya, da musaya a fannonin tattalin arziki daban daban.

A nahiyar Afirka ma, masana da dama na da yakinin cewa, kasashen nahiyar za su ci babbar gajiya daga wannan shawara, kuma akwai bukatar amfani da wannan dama, don hada kai da kasar Sin ta fannin aiwatar da shawarar yadda ya kamata.

A karshen watan Afrilun bana ma an gudanar da taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A yayin wannan taro, darektan zartaswa na sashen nazarin harkokin Najeriya, a cibiyar nazarin batutuwan Afirka dake jami'ar horas da malamai a lardin Zhejiang na kasar Sin, Dr. Ehizuelen Michael ya bayyana cewa, "ziri daya da hanya daya" ta zamo shawara da ta bunkasa mu'amala, da cudanya tsakanin kasashe da yankuna daban-daban a fadin duniya, kana shawara ce dake samar da wani sabon salon hadin-gwiwar kasa da kasa mai kawo moriyar juna.

Tuni dai aka riga aka samu sakamako mai armashi a fannin aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" a kasashen Kenya, da Djibouti, da Masar, da wasu kasashen Afirka.

Bugu da kari a kokarin ta na fadada hadin gwiwa da sauran sassan duniya, wajen samar da damammaki na zuba jari daga waje, da gina kyakkyawan yanayi, wanda zai ba da damar takara a mataki na kasa da kasa, Sin ta kira taron baje kolin tattalin arziki da cinikayya na farko tsakanin ta da kasashen Afrika a birnin Changsha, fadar lardin Hunan dake yankin tsakiyar kasar Sin.

Yayin taron da ya gudana a watan Yunin bana, cikin sakon da ya aike ga taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, an kirkiro baje kolin ne, wanda aka sanar da tanadar sa yayin taron kolin Beijing na tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika ko (FOCAC) da aka yi a watan Satumban bara, domin samar da dandalin zurfafa hadin gwiwar bangarorin biyu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

Baje kolin tattalin arziki da cinikayyar na farko tsakanin Sin da Afrika, ya hada gwamnatocin bangarorin biyu, da masana, da 'yan kasuwa da cibiyoyin hada-hadar kudi, domin tattauna manyan ayyukan hadin gwiwa domin cimma moriya tare.

Ana dai iya shaida cewa, karkashin wadannan kudurori na Sin, na kara bude kofa da cudanyar cinikayya, da hada hadar zuba jari, sassan duniya za su ci gajiya ta fuskar shiga karin kasuwannin kasar Sin mafiya yawan al'umma a duniya. Kaza lika ta wannan kafa, kasar Sin ta samar da damar cudayya tsakanin ta da karin kasashe a fannonin da a baya, ba a bayar da dama a shiga don zuba jari ba.

Har ila yau, wadannan tanade tanade, sun samar da damammaki musamman ga kasashe masu tasowa ciki hadda na nahiyar Afirka, na cin moriya daga dunbin ayyukan more rayuwa, da sanin makamar aiki, da damammaki na bincike da raya ilimi, da musayar fasahohi, da kirkire kirkire, da karin guraben ayyukan yi da ake samu, a fannonin da Sin ke da fifiko.

A karshe akwai fatan cewa, al'ummun duniya za su yi cudanya da kasar Sin, wajen cin gajiyar bai daya, karkashin matakan da kasar ke ci gaba da aiwatarwa, don ganin an inganta yanayin zuba jarin waje, wanda zai ba da damar takara a mataki na kasa da kasa. (Marubuci: Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China