Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi:Abin da Amurka ta shuka shi za ta girba
2019-08-21 21:29:58        cri
Kwanan nan, shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosida, da dan majalisar dattawan kasar Marco Rubio suka furta karara cewa, za su yi kokarin ganin an zartas da shirin dokar kare hakkin dan Adam da dimokuradiyya ta Hong Kong bayan da aka farfado da taron majalisar dokoki, furucin da suka bayyana goyon baya ga masu nuna karfin tuwo a Hong Kong wajen aikata laifuka, a yunkurinsu na haddasa rikici da barna a Hong Kong.

A hakika, wasu manyan jami'an gwamnatin Amurka da kuma hukumomin da suka hada da hukumar leken asiri ta kasar suna mara baya ga masu tsattsauran ra'ayi a Hong Kong, wadanda baya ga saduwa da 'yan aware na Hong Kong, suna kuma ba su kudade da ma shawara, har ma suka yi barazanar alakanta batun Hong Kong da batun takaddamar cinikiyya dake tsakanin Amurka da Sin.

Tun a watan Yunin wannan shekara, masu tsattsauran ra'ayi da nuna karfin tuwo sun kaiwa 'yan sanda hari, da kuma dukan 'yan jarida da masu yawon shakatawa, har ma sun wulakanta tutar kasar Sin da tambarin kasar da na yankin musamman na Hong Kong, sun kuma toshe hanyoyi da kawo tseko a filin jirgin saman yankin…

A game da wannan, tsohon babban editan jaridar Wirtschaftswoche ta kasar Jamus, Stefan Baron ya wallafa wani sharhi a jaridar Handelsblatt, inda ya ce, "Idan irin haka ya faru a kasar Amurka, da tuni an kawo karshen tarzomar."

Bai kamata wasu 'yan siyasa da masu kin jinin kasar Sin su rika raina aniyyar gwamnatin kasar Sin da ma al'ummarta na kiyaye 'yanci da tsaro da dinkuwar kasar ba. Duk wanda yake neman lalata ci gaba da kwanciyar hankali a Hong Kong a yunkurin dakile ci gaban kasar Sin, lalle hakarsa ba za ta cimma ruwa ba. Sai dai ma kaikayi ya koma kan mashekiya. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China