Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ba za ta ci cimma makarkashiyar hada batun tattalin arziki da ciniki da manufar siyasa ba
2019-08-20 21:15:58        cri
Jiya Litinin mataimakin shugaban kasar Amurka Michael Pence ya gabatar da wani jawabi yayin taron muhawara na dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin na Detroit Economic Club, inda ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana martaba jama'ar kasar Sin matuka, kuma ba ta son kasuwar kasar Sin ta yi hasara, amma idan sassan biyu, wato Sin da Amurka za su daddale yarjejeniyar tattalin arziki da cinkyayya a tsakaninsu, to dole ne kasar Sin ta cika daukacin alkawuran da ta dauka, ciki har da alkawarin bin cikakken tsarin dokoki na Hong Kong bisa hadaddiyar sanarwar Sin da Birtaniya, wadda suka daddale a shekarar 1984.

Furucin mataimakin shugaba Michael Pence ba shi da tushe ko dalili ko kadan. An lura cewa, ya hada batun cinikayya da manufar siyasa, har ya fito fili ya tsoma baki cikin harkokin gida na kasar Sin, da nufin matsa lamba ga gwamnatin kasar Sin.

Idan an waiwayi abubuwan da suka faru yayin tattaunawar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka a cikin shekara daya da ta gabata, za a fahimci cewa, dalilin da ya sa sassan biyu suka gamu da matsala shi ne, gwamnatin Amurka ba ta cika alkawarin da ta dauka ba, har ta dauki matakin kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin, amma a sa'i daya kuma ta bayyana cewa, tana martaba jama'ar kasar Sin matuka, haka kuma ba ta son kasuwar kasar Sin ta yi hasara. Hakika furucin wasu 'yan siyasar Amurka kamar Michael Pence, bai dace da matakin da suka dauka ba. Ko shakka babu al'ummun kasar Sin ba sa jin dadi kan wannan batu, saboda ba su ga sahihanci ko kadan daga wajen gwamnatin Amurka ba.

A sa'i daya kuma, kamata ya yi mataimakin shugaba Michael Pence ya waiwayi tarihi, don ganin kuskuren dake cikin maganarsa game da batun Hongkong. A cikin jawabinsa, ya ce, hadaddiyar sanarwa tsakanin Sin da Birtaniya ta kasance wata takardar siyasa da bangarorin biyu suka kulla a shekarar 1984 kan maido da ikon kasar Sin a yankin Hongkong da dai sauran abubuwa da za a gudanar a lokacin wucin gadi. Bayan da kasar Sin ta maida ikonta kan yankin Hongkong a hukunce a ranar 1 ga watan Yulin shekarar 1997, abubuwan da aka tanada a cikin sanarwar game da hakki da nauyin da Birtaniya ke da shi a Hongkong sun kare, kuma sanarwar ta zama wani fayil na tarihi. Daga nan kuma, Sin ta gudanar da harkokin Hongkong bisa tsarin mulkin kasar da kuma doka ta musamman na yankin Hongkong. A matsayin mataimakin shugaban Amurka, ya tsoma baki kan harkokin cikin gidan kasar Sin bisa wani fayil da aka daina amfani da shi, lamarin da ya kasance na ban dariya, da ya baiwa mutane mamaki tare da rage mutuncin Amurka a duniya.

Amurka tana alakanta batun Hong Kong da yarjejeniyar tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Amurka, har ma ta yi shelar sayar wa Taiwan jiragen saman yaki kirar F-16V wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 8. Haka kuma ta soke wasu shafukan sada zumunta na Twitter da Facebook da suka mara wa gwamnatin kasar Sin baya kan batun Hong Kong. Dalilin matsawa kasar Sin lamba haka shi ne, domin ta yi matukar bakin cikin ganin takaddamar ciniki da ta tada kan kasar Sin ba ta ci nasara ba, kana kuma, ta yi matukar damuwa da tsoro da ganin karuwar barazanar koma-bayan tattalin arzikinta.

Ana iya gano cewa, a cikin shekara fiye da daya da ya gabata tun bayan da Amurka ta kaddamar da takaddamar cinikayya tsakaninta da Sin, Sin tana raya tattalin arzikinta yadda ya kamata. Amma tattalin arzikin Amurka na fuskantar matsalar tabarbarewa. Musamman ganin yadda yawan ribar da aka samu ta hanyar sayen takardun lamuni na Amurka na shekaru biyu ya fi na shekaru 10, a idanun masu zuba jari, lamarin ya kasance wata alama ta tabarbarewar tattalin arzikin Amurka. Ko da yake Peter Navarro, Lawrence Kudlow da Michael Pence sun sha yin kalamai a kwanakin baya cewar, wai ba su gano tabarbarewar tattalin arzikin Amurka ko kadan ba, amma kalamansu ba su iya hana tawayar kasuwa ba. Bisa la'akari da yanayin da kasarsu ke ciki ta fuskokin tattalin arziki da siyasa, sun kara matsawa kasar Sin.

Amma, a cikin shekara daya ko fiye da suka gabata, abubuwa sun shaida cewa, matsa wa kasar Sin lamba mafi tsanani ba ta yi amfani ba ko kadan ba, a maimakon haka, ta tsananta halin da ake ciki a lokacin da ake kokarin kawar da matsaloli. Bangaren Sin ya tsaya kan matsayinsa na cewa, a lokacin da ake tattaunawa kan batun cinikayya, bai kamata a shigar da sauran batutuwa a ciki ba. Bangaren Sin yana son tattaunawa da bangaren Amurka bisa ka'idojin zaman daidai wa daida da mutunta juna, amma a kan wasu muhimman batutuwa, ba zai yi rangwame ko kadan ba. A 'yan kwanakin baya, ofishin wakilin cinikayya ta kasar Amurka ya sanar da cewa, zai buga karin harajin kwastam da kaso 10 cikin dari kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 300, da za a shigar da su kasar Amurka. Sabo da haka, babu sauran hanyar da bangaren Sin zai iya zaba, sai dai ya dauki hakikanan matakan mayar da martani, domin sake bayyana niyyarsa ta kare babbar moriyar kasar Sin da moriyar al'ummarta.

Kasar Sin ba za ta lalata moriyar sauran kasashen duniya domin neman ci gaban kanta ba, amma ba za ta yi watsi da halaltacciyar moriyar kanta ba. Kada kowa ya yi fatan kasar Sin za ta amince da matakan da za su lalata moriyarta, duk wanda yake son mayar da batun cinikayya zuwa ta siyasa, to zai sha kaye.(Masu fassara:Jamila, Amina, Tasallah, Kande, Sanusi)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China