Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na da imanin kiyaye muradunta yayin takaddamar ciniki tsakaninta da Amurka
2019-08-19 15:14:51        cri

Wasu masanan kasar Sin sun bayyana ra'ayinsu a birnin Beijing a kwanan baya, cewar kasar Amurka ta tada takaddamar ciniki a tsakaninta da kasar Sin, amma ba ta da karfin yin takaddamar cikin dogon lokaci. A bangaren Sin kuwa, ko da yake ba ta son shiga takaddamar cinikin, amma tana da imanin kiyaye muradunta, ko da yake Amurka ta sha sabawa alkawarinta.

Game da kudurin Amurka na kara yawan haraji da kaso 10 kan kayayyakin da Sin za ta fitar zuwa Amurka, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 300, shugaban kwamitin kula da ka'idojin harajin kwastan na majalisar gudanarwar kasar Sin ya bayyana cewa, wannan kudurin da Amurka ta tsayar ya sabawa ra'ayi bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a kasar Argentina da birnin Osaka na kasar Japan, wanda ya kauce hanyar daidaita matsala yadda ya kamata. Don haka babu yadda za a yi, illa Sin ta dauki matakin da ya wajaba domin mayar da martani.

A yayin taron kara wa juna sani kan batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda aka shirya a Beijing a kwanan baya, tsohon karamin jakadan Sin ta fuskar kasuwanci da ke birnin San Francisco da New York na kasar Amurka Mr. He Weiwen, ya gabatar da kididdigar shige da fice ta Amurka a farkon rabin shekarar bana, inda ya bayyana cewa, takaddamar cinikin da Amurka ta kaddamar ta kawo illa ga tattalin arzikinta. He ya kara da cewa,

"Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwancin Amurka ta fitar, an ce, jimillar kudin kayayyakin da Amurka ta fitar zuwa Sin a farkon rabin bana ta ragu da biliyan 12.1. Kuma sabo da Amurka ba ta fitar da karin kayayyaki zuwa ga sauran yankuna ba, adadin kudin harajin fitar da kaya zuwa sauran kasashen duniya na Amurka ya ragu da kashi 0.9 cikin dari bisa na bara. Kuma sakamakon wannan matsala, jimillar karuwar GDP da Amurka ta samu daga Afrilu zuwa Yuni ta kai kaso 2.1, wanda aka yi hasashen ganin jimillar ta kai kaso 2.7."

A nasa bangaren kuma, Mei Guanqun, mataimakin manazarci a ofishin nazarin tattalin arzikin duniya da ke cibiyar cudanyar tattalin arziki tare da kasashen duniya ta kasar Sin ya yi hasashen cewa, Amurka na fuskantar matsalar rashin daidaito a tsakanin tattalin arziki na hadaka, da wanda ke gudana ta yanar gizo, a tsakanin kashe kudade da adana su da dai sauransu. Amma domin magance matsalar, dabarar da gwamnatin Amurka ta fitar ita ce dora matsalar a kan wata kasa daban. Mei ya nuna cewa, Amurka ba ta da karfin yin takaddamar cinikin cikin dogon lokaci.

"Tattalin arzikin Amurka zai samu tabarbarewa nan ba da jimawa ba. Amma a cikin wannan yanayin da take ciki, idan Amurka ta ci gaba da daukar matakin kara sanyawa kayayyakin Sin na dala biliyan 300 kudin haraji da kaso 10, to yanayin tattalin arzikin Amurka zai kara tsananta. Don haka muna iya ganin cewa, Amurka ba ta da karfin ci gaba da takaddamar ciniki a tsakaninta da Sin, yadda lamarin zai ci gaba yana hannun kasar Sin."

Jiang Yuechun shi ne shugaban cibiyar nazarin tattalin arzikin duniya, da ci gabansa, da ke kwalejin nazarin harkokin kasa da kasa ta kasar Sin. A ganinsa, Sin ba ta son shiga cikin takaddamar cinikin, amma idan akwai takaddamar, to, Sin ba ta jin tsoron komai. Ya ce Sin na kokarin daidaita matsalar zuwa damar samun bunkasuwarta. Jiang yana mai cewa,

"A fannin bude kofa ga waje, Sin ta fitar da matakai hudu, da matakai takwas daya baya daya, tun daga shekarar bara har zuwa yanzu. Matakan da suka kasance wadanda ba a taba zatonsu a baya ba. Wani shiri ne da Sin ta tsara domin kyautata aikin bude kofa ga waje, bayan da ta yi nazarin fasahohin da ta samu a wannan fanni a cikin shekaru 40 da suka gabata. Don haka ina da imanin cewa, bayan da Sin ta daidaita manufofi don kara bude kofa ga waje, muna da karfi na samun nasara har zuwa karshe. "

Zhang Jianping, wani jami'in ma'aikatar kasuwancin Sin ya nuna cewa, Sin cibiya ce mafi girma a duniya ta fuskar masana'antu, kuma kasa ce mafi girma wajen cinikayyar kayayyaki, wadda ta kasance abokiyar ciniki mafi girma ga kasashe fiye da 130. Haka kuma ana kokarin gano sirrin cinikayya tsakanin Sin da kasashen da shawarar "ziri daya da hanya daya" ta shafa. Don haka yana ganin cewa, Sin na da imani wajen tattalin arzikinta, ba ta tsoron takaddamar ciniki a tsakaninta da Amurka. Sin ta kuma bukaci kasar Amurkar da ta nuna sanin ya kamata, wajen neman hanyar samun bunkasuwarta yadda ya kamata.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China