Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dole a yanke wa kamfanin FedEx hukunci bisa laifin da ya aikata
2019-08-18 20:32:58        cri

'Yan sanda birnin Fuzhou na lardin Fujian dake kudancin kasar Sin sun samu rahoton cewa, wani kamfanin cinikin kayan wasan motsa jiki na lardin ya samu sakon da wani dan kasuwar Amurka ya aika masa ta kamfanin aika sakwanni na FedEx na Amurka, wanda ke kunshe da bindiga. Wannan wani mummunan laifi ne na daban da kamfanin na FedEx ya aikata bayan da hukumomin shari'ar kasar Sin suka fara gudanar da bincike a kansa bisa doka.

Tun shekaru sama da talatin da suka wuce, kamfanin aika sakwanni na FedEx na Amurka ya fara shiga kasuwar kasar Sin, wanda dole ya san dokoki gami da ka'idojin kasar sosai. Amma, tun da gwamnatin Amurka ta sanya kamfanin sadarwa na Huawei na kasar Sin a cikin jerin kamfanonin da ta takaitawa shigar da kayansu kasar a watan Mayun bana, ya zuwa yanzu, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba FedEx ya shirya makarkashiya a kan kayan kamfanin Huawei, al'amarin da ya sa ake ta shakkun cewa FedEx da gwamnatin Amurka, jirgi daya ne ya kwaso su.

Lokacin da hukumomin dokokin kasar Sin ke gudanar da bincike kansa, kamfanin FedEx ya kara aikata wannan mummunan laifin na shigowa da bindiga cikin kasar Sin, abun da ya nuna cwa, a matsayin hamshakin kamfanin aika sakwanni a Amurka, irin aika-aikar da FedEx ya yi ta keta hakkokin wadanda suka yi amfani da hidimomin kamfanin, da kawo babbar barazana ga tsaron kasar Sin, da keta dokoki gami da ka'idojin kasar, abun da ya kasance wani mummunan laifin da kamfanin ya aikata da gangan. Kasar Sin kasa ce mai zaman doka da oda, kuma kamata ya yi duk wani kamfani ko dan Adam na kasashen waje dake kasar Sin ya bi dokar kasar.

A halin yanzu 'yan sandan birnin Fuzhou sun riga sun kwace bindigar da kamfanin ya shigo da ita kasar, da fara gudanar da bincike kan lamarin. Ya zama tilas kamfanin na FedEx ya bada hadin-kai ga 'yan sandan kasar Sin don amsa laifin da ya aikata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China