Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takardar bayani ta wanke karairai 3 game da aikin koyar da sana'o'i da ake yi a jihar Xinjiang
2019-08-16 21:07:14        cri

A yau Juma'a, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani game da yadda ake koyar da sana'o'i a jihar Xinjiang. A cikin wannan takarda, an yi wa al'ummun duniya bayanai filla filla game da dalilin da ya sa aka kafa cibiyoyin koyar da sana'o'i da abubuwan da ake koyarwa a cikin cibiyoyin, da kuma sakamakon da aka samu a wadannan cibiyoyi. A cikin takardar, an yi amfani da shaidu masu tarin yawa domin karyata karairai uku da wasu mutane daga kasashen yammacin duniya suka yi domin bata sunan cibiyoyin, an kuma bankado hakikanin burinsu na neman tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da sunan "hakkin bil Adama" da kuma ma'aunoni iri biyu.

Alkaluman da aka fitar, sun nuna cewa, tun daga shekarar 1990 zuwa karshen shekarar 2016, 'yan aware da masu tsattsaurar ra'ayin addinai da wasu kungiyoyin ta'addanci sun tayar da dubban matsalolin nuna karfin tuwo da aikata ta'addanci a jihar Xinjiang, wadanda suka lalata yanayin zaman lafiyar da ake ciki a yankin Xinjiang da ma tattalin arzikin yankin. An dauki matakan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar yankin Xinjiang, da kuma dakile ko tsoratar da 'yan ta'adda ne domin nuna namijin kokarin kare da kuma kiyaye hakkin bil Adama na al'ummar yankin Xinjiang.

Dalilan da suka sanya kafa cibiyoyin koyar da sana'o'i a yankin Xinjiang bisa doka kamar yadda wasu kasashe da yankuna na kasa da kasa suke yi su ne, kokarin hana wasu kananan laifufukan tun kafin su zama manyan laifufuka, sannan za a iya dakile ta'addanci da kuma kyautata zaman rayuwar al'umma. Sabo da haka, wannan mataki ya yi daidai da babbar ka'idar dakile ta'addanci da kuma kawar da tsattsaurar ra'ayi kamar yadda kusan dukkan kasashen duniya suke dauka.

Dangane da wannan aikin, an bayyana hakikanin abubuwan da suka abku a cikin takardar bayanin, ta yadda aka karyata zargin da wasu kasashen yammacin duniya ke yi kan ayyukan cibiyar koyar da sana'o'i da ake gudanar da su a jihar Xinjiang.

Da farko dai, cibiyoyin koyar da sana'o'i da aka gina a jihar, makarantu ne, ba wai "gidan kaso" ko "kurkuku" kamar yadda kasashen yamma suka bayyana su ba.

Ban da haka, hanyar da ake bi wajen gudanar da aikin koyarwa cikin cibiyoyin ita ce, koyar da wadanda ke cin gajiyar shirin koyon sana'o'i a cikin makarantu, domin su koyi fasahohi, su kuma gwada su. Ana koyar da sana'o'i ne kyauta, ta yadda za a nisanta matasa da tsattsauran ra'ayi, gami da taimaka musu samun ilimi da fasahohi. Ana kuma girmama 'yanci da hakkin masu koyon sana'a, gami da kokarin tabbatar da su a cikin cibiyoyin.

Haka zalika, babu aikace-aikacen neman "kau da al'adun kabilar Uygur da na wasu kabilun" ko kadan a cikin cibiyoyin. Kafin a shiga wannan cibiyoyin, sai an duba tarihin aikata laifuka, wato za a bincika ko mutum ya taba aikata wani ta'addanci, ko yana da ra'ayi na kaifin kishin addini, ko kuma ya taba aikata wasu laifuka, ba tare da la'akari da kabilarsa, ko yankin da ya fito, ko kuma addinin da yake bi ba.

A kokarin da ake na ganin bayan ta'addanci, da kau da tsattauran ra'ayi a jihar Xinjiang, an tsara wasu darusa a cikin cibiyoyin koyar da sana'o'i, wadanda suka hada da darasin koyon yaren gama gari a kasar Sin, da ilimin dokoki, da na koyon sana'a. Ta hanyar koyon darusan, dalibai sun samu ilimin da suke bukata domin dogaro da kai, da mu'ammala da mutanen sauran kabilu, da kuma sabawa da zaman rayuwar zamani. A sa'i daya kuma, an ba su cikakkiyar girmamawa dangane da hakkinsu na amfani da harsunansu na uwa, gami da al'adarsu.

Na uku kuma, cibiyar koyar da sana'o'i ba ta danne addinai, ciki had da addinin Musulunci. cibiyar ta raba harkokin ba da ilmi daga harkokin addinai. Don haka masu koyon sana'o'i ba za su shirya da kuma shiga harkokin addinai a cibiyar ba, amma idan sun koma gida, suna iya yanke shawarar shiga halaltattun harkokin addinai ko a'a da kansu. Hakan ya nuna cewa, cibiyar tana girmama 'yancin masu koyon ilmin sana'o'i na bin addini.

Sakamakon kafuwar cibiyar da sauran matakai masu ruwa da tsaki, ya sa ba a samu rahotannin aukuwar hare-haren ta'addanci a jihar ta Xinjiang a cikin shekaru 3 da suka gabata ba. A watanni shida na farkon shekarar bana, yawan matafiya na cikin gida da wajen kasar Sin da suka ziyarci Xinjiang ya wuce miliyan 75, wanda ya karu da kaso 46 bisa na shekarar bara. Akwai kyakkyawar alamar ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma a Xinjiang.

Matakai masu ruwa da tsaki da kasar Sin ta dauka a Xinjiang sun kuma samar da kyawawan fasahohin yaki da ta'addanci da kau da tsattsauran ra'ayi a duniya. Kwanan baya, jakadu daga kasashe fiye da 50 sun aika da wata wasika da suka sa hannu a kai ga shugaban kwamitin kula da kare hakkin dan Adam na MDD da manyan kwamishinoni masu kula da hakkin dan Adam, inda suka goyi bayan matsayin Sin kan batun Xinjiang. Hakan ya nuna cewa, an fahimci kasar Sin ta kuma samu goyon baya daga kasashen duniya dangane da batun Xinjiang.

Don haka, bai dace wasu mutane daga kasashen yammacin duniya su rika yi wa kasar Sin bahaguwar fahimta ba, su daina nuna fuska biyu, su kuma karanta wannan takardar bayani a tsanake ta yadda za su fahimci gaskiya. Su daina kalaman suka da babu hujjoji a cikinsu ba da bata kokarin da kasar Sin take yi wajen kau da tsattsauran ra'ayi a Xinjiang. Jihar ta Xinjiang mai wadata da kwanciyar hankali za ta kawar da duk wata jita-jita da wasu ke yadawa kan nasarar da kasar Sin ta samu a ayyuka yaki da ta'addanci. (Sanusi, Bello, Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China