Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar al'adun Sin dake Mauritius
2019-08-16 13:23:16        cri

An kaddamar da cibiyar nuna al'adun kasar Sin a Port Louis, fadar mulkin kasar Mauritius a watan Yulin shekarar 1988, cibiyar da take kasancewa cibiyar nuna al'adun da kasar Sin ta kafa a kasashen ketare.

Tun bayan da aka kafa cibiyar nuna al'adun kasar Sin a Port Louis, fadar mulkin kasar Mauritius a watan Yulin shekarar 1988, cibiyar tana kara habaka sannu a hankali a cikin shekaru sama da 30 da suka gabata, har tana kara kawo tasiri a kasar ta Mauritius, haka kuma tana taka babbar rawa wajen cudanyar al'adun dake tsakanin kasashen biyu.

Cibiyar nuna al'adun kasar Sin mai fadin muraba'in mita 9600 tana kudu maso yammacin birnin Port Louis, wadda ta kasance cibiyar nuna al'adun da gwamnatin kasar Sin ta kafa a kasashen ketare, darektan cibiyar Song Yanqun ya gaya mana cewa, dalilin da yasa gwamnatin kasar Sin ta kafa cibiyar nuna al'adunta ta farko a kasar ta Mauritius shine domin kasar tana da kabilu da dama wadanda ke zaman jituwa yadda ya kamata, kana al'adu iri daban daban dake kasar su ma suna cudanya cikin lumana, ban da haka, Sinawa makaurata sun riga sun fara rayuwarsu a kasar kafin shekaru 200 da suka gabata, a don haka ana iya cewa, cudanyar al'adun dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Mauritius tana da tushe mai inganci, darekta Song Yanqun yana mai cewa, "Sinawa masu kwazo da himma sun yi kokari matuka daga zuriya zuwa zuriya a kasar Mauritius, har kullum suna gada da kuma yada al'adun gargajiyar kasar Sin, har al'adun kasar Sin sun samu karbuwa daga wajen 'yan siyasa da bangarori daban daban na kasar, Mauritius kasa daya kacal dake nahiyar Afirka wadda take mayar da bikin bazara na gargajiyar kasar Sin a matsayin ranar bikin kasar, a bayyane an lura cewa, al'adun kasar Sin sun samu karbuwa sosai daga wajen al'ummun kasar ta Mauritius."

A cikin shekaru 30 da suka gabata, cibiyar nuna al'adun kasar Sin ta samu ci gaba a bayyane, misali tana gudanar da ayyukan nuna al'adun gargajiyar kasar Sin da kwas din horas da ilmomi ga al'ummun kasar ta Mauritius, yanzu haka ana koyar da Sinanci da wasan Kungfu da raye-raye da kayan kide-kiden gargajiyar kasar Sin da zane-zane da rubutun kalmomin Sinanci da sauransu a cibiyar, a sa'i daya kuma, an shirya wasu ayyukan nuna al'adun kasar Sin na musamman kamar su "bikin bazara mai farin ciki" da "makon nuna al'adun kasar Sin" da "bikin tseren kwale-kwale" da "bikin tsakiyar kaka" da "makon nuna fina-finan kasar Sin" da sauransu, duk wadannan sun samu karbuwa matuka daga wajen al'ummun kasar ta Mauritius。

darekta Song Yanqun ya gaya mana cewa, "A shekarar 2018, mun taba shirya yawon keken furanni yayin da muke taya murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, bama kawai Sinawa dake kasar Mauritius sun shiga bikin bane, har ma kungiyoyin musulmai da kungiyoyin 'yan asalin Indiya su ma sun halarci bikin da muka shirya, mutane sama da dubu goma sun taru ne a Port Louis, a wancan lokaci, na yi alfahari matuka saboda mu Sinawa ne."

Kawo yanzu cibiyar nuna al'adun kasar Sin ta riga ta kasance muhimmin dandalin da ake samarwa al'ummun kasar Mauritius domin su kara fahimtar al'adun kasar Sin, har wasu daga cikinsu sun nuna babbar sha'awa da kauna ga al'adun kasar Sin.

Li Weisheng, 'dan asalin kasar Sin wanda aka haife shi a Mauritius shine dalibin kwas din horas da wasan Kungfu na farko da aka shirya a shekarar 1988, ya fara koyon wasan Kungfu ne a shekarun haihuwarsa na 16, ya gaya mana cewa, ya koyi basirar Sinawa daga wasan Kungfu, yana mai cewa, "Ina son koyon al'adun dake da nasaba da al'adun kasar Sin, shi yasa na je cibiyar nuna al'adun kasar Sin don koyon wasan Kungfu, ina ganin cewa, wasan Kungfu ba wasa bane kawai, shi ma salon rayuwa ne, na koyi hali na gari daga wasan."

Ko shakka babu cibiyar nuna al'adun kasar Sin ta samu babban sakamako, musamman ma a bangaren yada al'adun kasar Sin da ingiza cudanyar al'adun dake tsakanin kasar Sin da Mauritius.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China