Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Kawo karshen tashe-tashen hankula zai iya kubutar da kyakkyawan muhallin kasuwanci na Hong Kong
2019-08-15 20:29:13        cri

Yanzu haka bata gari na daukar matakai dake tsananta yanayi a titunan yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, matakin da ke lalata zaman lafiyar yankin.

Aikace-aikacen nuna karfin tuwo marasa kyau, sun sanya Hong Kong ya tsunduma cikin tashe-tashen hankula. A matsayinsa na daya daga cikin rukunoni mafiya karfin yin takara a duniya, yanzu haka an sanya Hong Kong shiga yanayi na hadari. Da gangan an lalata kyakkyawan muhallin kasuwanci da aka dade ana jinjina.

Abubuwan da masu zanga-zanga masu tsattsauran ra'ayi suka yi sun wuce iyakar dokoki, laifuffuka ne suke aikatawa, har ma akwai alamar ta'addanci. Abubuwan da suka yi sun saba wa dokokin Hong Kong da odar zamantakewar al'umma, sun kuma kawo barazana ga tsaron lafiyar mazauna yankin, da na matafiya, da kuma tsaron dukiyoyinsu, kana kuma sun illata kwanciyar hankali da wadatar Hong Kong, da kuma ci gaban tattalin arzikinsa, sun kuma raunana kyakkyawar surar Hong Kong a duniya.

Kyakkyawan muhallin kasuwanci, ginshiki ne na Hong Kong wajen samun ci gaba. Amma aikace-aikacen bata gari suna illata muhallin kasuwancin Hong Kong, tare da raunana karfin zuciyar kasa da kasa kan yankin na Hong Kong. Idan ba za a dauki matakai masu karfi na kawo karshen nuna karfin tuwo ba, hakan zai illata ga ci gaban Hong Kong.

Kawo karshen tashe-tashen hankula, abu ne na gaggawa da tilas a aiwatar domin ceton Hong Kong. Ba za a bari masu bore su rushe kuzarin Hong Kong ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China