Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan kasa da kasa sun yi Allah wadai da bore da aka tayar a Hong Kong tare da yin kira da a gaggauta dawo da oda a yankin
2019-08-15 13:42:48        cri

Masanan kasa da kasa sun bayyana rashin jin dadinsu matuka game da ayyukan keta doka da tsegaru suka yi a Hong Kong kwanan baya, saboda ayyukan sun lalata makoma da zaman lafiyar yankin, don haka suka yi kira da a gaggauta dakatar da tada zaune tsaye tare da dawo da doka da oda a yankin.

Shugaban asusun Kuhn Robert Lawrance Kuhn ya ce, ayyukan masu zanga-zanga sun sa an katse harkoki a filin saukar jiragen saman yankin, hakan ya sa aka dakatar tashi da saukar jirage, babu wata kasa da za ta yarda da faruwar irin wannan matsala. Ya kara da cewa, ba za a lamunci ci gaban wannan tashin hankali a yankin Hong Kong ba, lamarin ba ma kawai ya kawo illa ga jama'ar yankin ba, har ma ya kawo cikas ga bunkasuwar yankin.

Masanin nazari manufofin jama'a na kasar Kenya Stephen Ndegwa ya ce, halin da yankin ke ciki na kara tsananta, lamarin da ya kawo cikas ga jin dadin jama'a da bunkasuwar yankin, kuma mazaunan wuri su ne matsalar za ta fi shafa. Ya kamata, a dauki mataki cikin gaggawa don dakatar da rikicin, a zakulo tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifi a gaban kuliya.

Wani masani na kasar Sudan ya ce, boren da aka tayar a Hong Kong ya saba tsarin zamantakewa, abin da ke nuna cewa, akwai hannun wasu kasashe a ciki. Ya ce, yana goyon bayan duk matakin da gwamnatin tsakiyar kasar Sin da kuma gwamnatin yanki na musamman na Hong Kong suke dauka na dakile masu bore tare da gaggauta dawo da doka da oda da kwanciyar hankali a yankin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China