Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Sin: Ya dace a sake tsara tsarin hada-hadar kudin duniya
2019-08-15 11:04:14        cri

Jiya Laraba a nan birnin Beijing, mamban sashen ilmi na cibiyar nazarin kimiyyar zaman takewar al'ummar kasar Sin kuma darektan ofishin nazarin hada-hadar kudi da raya kasa na kasar Li Yang ya bayyana cewa, hakika batun darajar kudi yana shafar takara a bangaren saurin ci gaban tattalin arziki, yana ganin cewa, Amurka ce ke kan gaba a tsarin hada-hadar kudin duniya, kuma ta dade tana daidaita darajar kudi, tana kuma amfani da darajar kudi domin hana ci gaban sauran kasashen duniya, a don haka ya dace a sake tsara tsarin hada-hadar kudin duniya da ake gudanarwa a halin yanzu.

A yayin taron kara wa juna sani game da "sake tsara sabon tsarin hada-hadar kudin duniya" da aka kira jiya a nan birnin Beijing, mamban sashen ilmi na cibiyar nazarin kimiyyar zaman takewar al'ummar kasar Sin kuma darektan ofishin nazarin hada-hadar kudi da raya kasa na kasar Li Yang ya bayyana cewa, ya dace a inganta tsarin hada-hadar kudin duniya da ake amfani da shi yanzu, idan an lura, za a ga an raba kasashen duniya gida biyu, wato masu taka rawa da kuma wadanda ba a kula da su, kana saboda yadda aka ba dalar Amurka wani muhimmin matsayi, shi ya sa har kullum kasar Amurka take kasancewa a kan gaba wajen tsara tsarin hada-hadar kudin duniya, kasashe wadanda ba a mayar da hankali a kan su a fannin suna yin manyan sauye-sauye bisa dalilin ci gaban tsarin tattalin arzikin duniya. Yayin da tsakanin shekarar 1988 zuwa 1994 Amurka ta ayyana kasashe ko yankuna 13 a matsayin masu rage darajar kudi, dalilin da ya sa haka shi ne domin wadannan kasashe ko yankuna sun samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri, masanin kasar Sin Li Yang ya yi nuni da cewa, lamarin ya nuna cewa, batun darajar kudi ya shafi takara a bangaren saurin ci gaban tattalin arziki, yana mai cewa, "Mun lura cewa, Amurka ta taba ayyana wasu kasashe ko yankuna kamar su Jamus da Japan da yankin Taiwan na kasar Sin da Koriya ta Kudu da sauransu a matsayin masu rage darajar kudi, duk domin saurin ci gaban tattalin arzikinsu ya fi na Amurkar, sannan ba ta amince da wannan hakan ba, Don haka ana iya cewa, batun darajar kudi, batu ne da ya shafi takara a bangaren saurin ci gaban tattalin arziki."

Li Yang yana ganin cewa, a tsarin hada-hadar kudin duniya na yanzu, ita kanta Amurka kasa ce dake rage darajar kudi, a cewarsa: "Darajar kudi makami ne mai karfi na nuna fin karfin dala, a don haka Amurka, kasa mai nuna fin karfin kudi tana haifar da babban tasiri ga sauran kasashen duniya, musamman ma kasashen da Amurka ta taba ayyanasu a matsayin masu rage darajar kudi, hakika Amurka ita ce kasa daya kacal wadda ke da karfin rage darajar kudi cikin dogon lokaci."

Shaidu sun ce, Amurka ta taba rage darajar kudinta har sau biyu a farkon shekarun 1970 ba tare da tattaunawa da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ko sauran mambobin asusun, a sanadin matakan da Amurka ta dauka, sun jefa daukacin kasashen duniya cikin mawuyacin hali na kusan tsawon shekaru biyar.

Alkaluman da wasu masanan Amurka suka fitar, sun nuna cewa, gwamnatin Amurka ta taba daukar mataki kan kasuwar darajar kudi har sau 1214 tsakanin ranar 2 ga watan Maris na shekarar 1973 zuwa ranar 19 ga watan Maris na shekarar 1997, yunkurin da ta cimma ya kai kaso 60 bisa dari, darajar kudi ta riga ta kasance makamin da take amfani da shi yayin da take hana ci gaban sauran kasashe. Li Yang y a ce, "Darajar kudi tana shafar bangarori biyu ko fiye, amma har kullum Amurka tana ganin cewa, ba ta da laifi ko kadan, laifin sauran kasashe ne kawai, a don haka darajar kudi ta kasance makamin da Amurka take amfani da shi yayin da take neman hana ci gaban sauran kasashe, idan an tantance ainihin amfanin makamin, za a lura cewa, wani yunkuri ne da ke yi Amurka domin kare moriyarta."

Li Yang ya kara da cewa, yanzu haka Amurka tana taka babbar rawa a cikin tsarin hada-hadar kudin duniya, tana iya ayyana sauran kasashen duniya a matsayin masu rage darajar kudi kamar yadda take so, shi ya sa ya dace a sake tsara tsarin yanzu, yana mai cewa, "Idan aka ci gaba da yin amfani da tsarin hada-hadar kudin duniya na yanzu wanda ya ba Amurka dama fiye da kowa ce kasa, hakan ba zai sa a kaucewa matakin da Amurka ta dauka kan darajar kudi ba, don haka ya dace a sake tsara tsarin hada-hadar kudin duniya, duk da cewa, kila zai yi wahala a cimma burin."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China