Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahauciyar guguwar Lekima ta shafi sama da mutane miliyan 12.8 a kasar Sin
2019-08-14 14:07:44        cri

Ma'aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar Sin ta bayyana cewa, ya zuwa karfe 4 na yammacin jiya Talata agogon kasar Sin, mahaukaciyar guguwar nan mai tafe da mamakon ruwa da iska da ake kira Lekima, ta shafi mutane kusan miliyan 12.88 a larduna 8 na kasar.

An kuma tsugunar da kimanin mutane miliyan 2 a lardunan Zhejiang, da Jiangsu, da Shandong da Anhui, da Fujian, da Liaoning da Jilin, da kuma birnin Shanghai. Baya ga gidaje kimanin dubu 13 da suka rushe wasu dubu 119 kuma suka lalace, da amfanin gona na kimanin eka dubu 996 da bala'in ya shafa.

Mahaukaciyar guguwar ita ce ta tara kuma mafi girma a wannan shekara, ta kuma halaka mutane 48 kana wasu 21 suka bace a lardunan Zhejiang da Shandong da Anhui. Koda yake mahaukaciyar guguwar ta fi yin mummunan barna a Zhejiang, inda ta fara sauka, ta kuma kashe mutane 39 kana wasu mutane 9 suka bace.

Hukumomin sun tura ma'aikatan ceto da na ba da agaji, da 'yan kwana-kwana, da sojoji da 'yan sanda da ma'aikatan hukumar lalubo wadanda suka bace.

A ranar Litinin, gwamnatin kasar Sin ta ware Yuan miliyan 300, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 42.66, don gudanar aikin ceto a lardunan Zhejiang da Shandong da Jiangsu.

A jiya Talata kuma, MDD ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, a shirye take ta taimakawa matakan da kasar take dauka na ganowa da na ceton, bayan lafawar mahaukaciyar guguwar ta Lekima. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China