Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afirka na bukatar dalar Amurka sama da tiriliyan 1.4 don cike gibin gidajen kwana in ji wani kwararre
2019-08-13 21:20:50        cri
Babban jagoran kamfanin gine gine na Shelter Afrique Mr. Andrew Chimphondah, ya ce nahiyar Afirka na bukatar kudi da yawan su ya kai dalar Amurka sama da tiriliyan 1.4, domin cike gibin gidajen kwana da al'ummar nahiyar ke bukata.

Mr. Chimphondah, ya ce nahiyar Afirka na fama da kamfar gidajen kwana masu nagarta sakamakon yawan karuwar al'ummar ta, da fadadar birane, da rashin managarcin tsarin birane, da kasuwar filaye maras inganci, da hauhawar kudaden kayan gini. Sauran su ne yaduwar sabbin yankuna awon igiya, da karancin tsare tsaren samar da kudade a fannin gine gidaje.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China