Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjeniyoyin Geneva sun cika shekaru 70 da samun amincewar duniya
2019-08-13 14:42:32        cri

A jiya ne yarjeniyoyin da aka cimma a Geneva game da doka da dabi'u da ka'idojin da suka shafi jin kai a lokacin yake-yake, suka cika shekaru 70, da duniya da amince da su.

Kungiyar ba da agajin jin kai ta kasa da kasa (ICRC) ta bayyana a shafinta na Intanet cewa, a ranar 12 ga watan Agustan shekarar 1949 ne, aka amince da yarjeniyoyin na Geneva, bayan yakin duniya na biyu.

Tun wancan lokaci, yarjeniyoyin suka kasance ginshikin dokar jin kai ta kasa da kasa kuma ake amfani da su wajen kare mutanen da yake-yake suka shafa a sassan duniya.

Kungiyar ICRC ta ce, yarjeniyoyin na Geneva, sun samar da daidaito mai muhimmnci tsakanin amfani da karfin soja da la'akari da batu na jin kai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China