Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mahaukaciyar guguwa ta rutsa da mutane kusan miliyan 9 a kasar Sin
2019-08-13 11:20:58        cri

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar Sin, ta ba da kididdiga cewa, ya zuwa karfe 4 na yammacin jiya Litinin, mahaukaciyar guguwa mai suna "Lekima" ta aukawa larduna 8 na kasar, ciki hadda Zhejiang, Jiangsu, Shandong, Anhui, Fujian, Hebei, Liaoning, Jilin da birnin Shanghai. Hukumar ta ce yawan mutanen da ta rutsa da su ya kai miliyan 8.97, sannan an tsugunar da mutane milyan 1.713 cikin gaggawa, daga cikinsu kuma, mutane miliyan 1.388 sun koma gidajensu lami lafiya.

An ba da labari cewa, hadarin ya haddasa mutuwar mutane 39 a lardin Zhejiang yayin da kawo yanzu ba a san duriyar wasu 9 ba. A Anhui kuma mutane 4 sun rasa rayukansu, sannan wasu 5 sun bace, kana a Shandong, Lekima ta halaka mutane 5, yayin da wasu 7 suka bace.

Ban da wannan kuma, wannan iftila'in ya lalata gidaje 5300, da gonaki hekta dubu 531. Ma'aikatan kwana-kwana fiye da dubu 30 ne suka shiga aikin ceto.

Hukumar kudi da hukumar agajin gaggawa ta kasar Sin sun kebe kudin tallafi RMB miliyan 300 a wannan rana ga lardunan Zhejiang, Jiangsu da Shandong don tallafawa aikin ceto da ba da kulawa ga wadanda hadarin ke rutsa da su. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China