Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi Sin da Japan su kara taka kyakkyawar rawa a al'amuran kasa da kasa
2019-08-12 19:30:20        cri

Kwanan baya, mataimakan ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Japan, sun shugabanci taron tattaunawa kan manyan tsare-tsare a birnin Nagano na Japan, inda kasashen 2 suka maido da gudanar da taron bayan shekaru 7.

A yayin taron, kasashen 2 sun tabbatar da aiwatar da muhimmin daidaito da shugabannin kasashen 2 suka cimma a yayin ganawarsu a wajen taron kungiyar G20 da aka yi Osaka, za su kuma yi kokarin kyautata huldar da ke tsakaninsu a sabon zamani. Lamarin ya nuna cewa, ana kyautata huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Japan sannu a hankali, bayan tangarda da aka fuskanta a baya.

Nan gaba kasashen 2 za su rika inganta amincewar juna ta fuskar siyasa, bisa ra'ayi daya da suka cimma a fannoni 10 na raya huldarsu, sa'an nan za su kara hadin gwiwar moriyar juna a fannonin yin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha, da kiyaye ikon mallakar ilmi, da zuba jari, da raya tattalin arziki da ciniki da dai sauransu. Har ila yau za su kyautata yin mu'amala ta fuskar al'adu, a kokarin kara azama kan cudanyar jama'ar kasashen 2.

Duk da haka, ya zuwa yanzu akwai wasu batutuwa da suka dade suna addabar kasashen 2. Don haka kamata ya yi kasashen 2 su daidaita wadannan batutuwan da ke jawo hankulansu yadda ya kamata, bisa ra'ayi daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma a Osaka, su kuma tinkari sabani ta hanyar da ta dace, a kokarin samar da muhalli mai kyau wajen raya huldar da ke tsakaninsu a sabon zamani.

A halin yanzu, ana fuskantar manyan sauye-sauye a duniya, don haka kamata ya yi kasashen Sin da Japan su kara taimakawa juna, da hada kai sosai a maimakon yin takara da juna, sa'an nan ana bukatar su yi kokarin kawo wa jama'arsu alheri, da kuma taka rawarsu a al'amuran kasa da kasa yadda ake bukata. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China