Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNIFIL ta yaba gudummawar da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suka bayar a aikin tone nakiyoyin da aka binne
2019-08-12 14:55:54        cri
Jagoran tawagar kai daukin gaggawa ta MDD dake kasar Lebanon(UNIFIL) De Reviers De Mauny, ya yaba da irin gudummawar da dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin ke baiwa tawagarsa da ma rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Jami'in ya bayyana hakan ne, lokacin da yake duba yadda dakarun na kasar Sin da aka tura yankin ke gudanar da aikin tone nakiyoyin da aka binne

A kwanakin nan, rukuni na 18 na sojojin injiniya na dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya na kasar Sin, ya yi aiki a wani fili da aka binne nakiyoyi dake kusa da yankin da MDD ta keba.

Kwamandan rukuni na 18 na dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin, Gao Chaoning, ya shaidawa Mauny cewa, a cikin shekaru 13 da suka gabata, dakarun kasar Sin dake aikin wanzar da zaman lafiya sun gudanar aikin tone nakiyoyin da aka binne ba tare wani ya jikkata ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China