Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin shugaban al'ummar Falasdinawa ya zargi Isra'ila da mamaye harabar masallacin Al-Aqsa
2019-08-12 11:40:45        cri
Kakakin shugaban al'ummar Falasdinawa Mahmoud Abbas, Nabil Abu Rudeineh, ya zargi gwamnatin Isra'ila da alhakin mamaye harabar masallaci mai tsarki na Al-Aqsa.

Cikin wani jawabi da kamfanin dillancin labarai na WAFA ya wallafa, Rudeineh ya ce, shugaba Abbas yana ci gaba da tuntubar bangarorin da abin ya shafa domin dakatar da dukkan mamayar da Yahudawa ke yiwa al'ummar Falasdinu da harabar masallaci mai tsarki, inda ya gargadi Isra'ila da kada ta kuskura ta mayar da rikicin siyasa zuwa na addini.

Harabar masallaci mai tsarki na Al-Aqsa, wanda Yahudawa ke gudanar da ibadarsu, ya kasance waje ne mai tsarki ga dukkan bangarorin mabiya addinan biyu, wato musulmai da Yahudawa.

A wannan shekarar, bikin sallar lahiya na mabiya addinin Islama ya zo daidai da ranar bikin hutun Yahudawa na Tisha B'Av, lamarin da ya sanya aka samu karuwar yawan Isra'ilawa masu ziyara zuwa wajen mai tsarki dake birnin Kudus.

Yankin masallacin na Al-Aqsa, yana daya daga cikin wuraren da aka fi samun yawan tashe-tashen hankula.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China