Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ayyukan jirgin dakon kaya na zamani na kasar Kenya ya kara fadada
2019-08-12 11:38:05        cri
Rahotanni daga kasar Kenya na cewa, layin dogo na zamani na kasar (SGR) da ya hade Mombasa da Nairobi, babban birnin kasar, yana gudanar da ayyukansa ba tare da wata matsala ba, tun lokacin da aka kaddamar da shi zuwa wannan lokaci, inda ya yi jigilar miliyoyin kayayyaki da fasinjoji.

A cewar masu kula da layin dogon, ya zuwa ranar 8 ga watan Agustan wannan shekara, jirgin ya yi kwanaki 800 yana aiki. Kana wani rahoto na cewa, ya zuwa ranar 31 ga watan Mayun wannan shekara, yawan fasinjojin da jirgin ya yi jigilar su, ya kai kimanin miliyan uku.

Daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Agustan wannan shekara, jirgin ya yi jigilar fasinjoji 949,000 tare da samar da hidima mai kyau. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China