Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wayon rage darajar kudi zai kawo illa ga duk duniya
2019-08-09 20:03:01        cri

Kwanakin baya baitulmalin kasar Amurka ya bayyana kasar Sin a matsayin "mai rage darajar kudi", matakin da ya sabawa ka'idojin da ake aiwatarwa tsakanin bangarori da dama, kana ya lalata matsayar da daukacin kasashen duniya suka cimma, irin wannan wayon da Amurka ke da shi ba ma kawai zai kawo illa ga kasashen duniya ba, har ma zai lalata moriyar kasar Amurka ita kanta.

A halin da ake ciki yanzu, wasu kasashe suna da makarkashiyar bangaranci da kuma ba da kariya ga harkokin cinikayyar kasashensu, a don haka daukacin kasashen duniya suke fuskantar kalubalen koma baya. A matsayinsu na manyan kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki a duniya, adadin GDP na kasar Sin da Amurka ya kai kaso 40 bisa dari na daukacin fadin duniya, shi ya sa huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasashen biyu tana shafar makomar ci gaban tattalin arzikin duniya.

Tun daga shekarar bara, gwamnatin Amurka ta fara daukar matakin kara sanya haraji kan kayayyakin da ake shigo da su daga kasar Sin, matakin ba ma kawai ya lalata huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu ba, har ma ya yi mummunan tasiri ga sauran kasashen duniya a bangarorin zuba jari da sayayya.

Kwanakin baya, baitulmalin kasar Amurka ya bayyana kasar Sin a matsayin "mai rage darajar kudi", zargin da ya sabawa ma'aunin manufar darajar kudin da ita kanta Amurkar ta tsara a shekarar 2016, ko shakka babu matakin zai kara lalata huldar dake tsakanin sassan biyu, har ma ya haifar da tangal-tangal a kasuwannin kudin duniya, ya kawo cikas ga harkokin cinikayyar dake tsakanin kasa da kasa da farfadowar tattalin arzikin duniya.

A irin wannan yanayi da ake ciki, wasu Amurkawa sun zargin kasar Sin a matsayin "kasa mai rage darajar kudi", sun yi hakan ne domin cin zalin tattalin arzikin kasar Sin, tare kuma da neman dalilin kara sanya haraji kan kayayyakin da ake shigo da su Amurka daga kasar Sin, kana suna son raya tattalin arzikin kasar ta hanyar matsa lamba ga asusun kota kwata na tarayyar Amurka domin ya rage ruwan kudin ajiyar banki, tare kuma da biyan bukatun siyasa a cikin kasar ta Amurka, amma burinsu ba zai cika ba.

Alal misali, Amurka ta saba matakin raya tattalin arzikin kasar ta hanyar sayar da kayayyaki masu araha, amma yanzu farashin kayayyakin da ake shigo da su Amurka daga kasar Sin ya karu, a don haka zai yi wahala kamfanonin Amurka su samu riba mai tsoka kamar yadda suke samu a baya, masu sayayya na Amurka ba su ji dadin hakan ba ko kadan.

Jaridar "Wall Street Journal" ta yi nuni da cewa, wayon rage darajar kudi zai kara lalata tattalin arzikin Amurka, saboda wannan matakin tamkar labarin rashin kunya ne da Amurka ta yada a kasuwar hada hadar kudi, shi ma zai haifar da hadari ga karuwar tattalin arzikin Amurka.

A shekarar 1997, kasashen Asiya sun gamu da rikicin hada hadar kudi, a shekarar 2008, daukacin kasashen duniya sun gamu da rikicin hada hadar kudi, yanzu haka musamman ma tun daga shekarar 2018, Amurka ta tayar da takaddamar cinikayya, amma har kullum kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan tsarin darajar kudi bisa bukatun kasuwa, ba ta taba yin takara ta hanyar rage darajar kudinta ba, amma tana daukar hakkinta na babbar kasar mai saurin ci gaban tattalin arziki bisa wuyanta, domin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba yadda ya kamata. Duk da cewa wasu Amurkawa sun yi zarginta cewar kasar Sin kasa ce mai rage darajar kudi, amma wannan wayon ba zai yaudari al'ummun kasashen duniya ba, sai ma ya haifar da koma bayan tattalin arzikin kasarsu, ya kuma zubar da kimar kasar Amurka ita kanta a idon duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China