Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin na cewa Sin na rage darajar kudinta ya nuna fuskoki biyu na Amurka
2019-08-09 11:23:33        cri


Ma'aikatar kudin Amurka ta ayyana kasar Sin a matsayin kasar dake rage darajar kudinta da gangan, abun da ba kawai ya sabawa ka'idojin da ita Amurka ta tsara da kanta ba, har ma ya yi biris da abun da gwamnatin Amurka ta yi na matsawa baitulmalin kasar lambar rage ruwan kudin ajiyar banki sau da dama. Hakan ya nuna irin wayon da Amurka ke da shi wajen cin zalin sauran kasashe.

Amurka ta dade tana amfani da darajar kudinta wato dala don nuna babakere da danniya kan sauran kasashe. Duk da cewa kasar Sin ta fara yin kwaskwarima ga tsarin kasancewar darajar kudinta wato RMB a shekara ta 1994, har yanzu akwai wasu mutanen Amurka wadanda suka rika matsawa kasar Sin lamba inda suka bukaci a samu hauhawa ko kuma faduwar darajar kudin Sin bisa halin da ake ciki. A baya-bayan nan, Amurka na yunkurin nuna bangaranci da tsananta takaddamar cinikayya tsakaninta da kasar Sin, al'amarin da ya kara haifar da tangal-tangal a kasuwannin kudin duniya, har ma darajar kudin Sin RMB ta dan ragu kadan. Nan take ita Amurka ta fara zargin gwamnatin kasar Sin tana mai cewa wai Sin na yunkurin rage darajar kudinta da gangan. Zargin nan abu ne mai ban mamaki kana ba shi da tushe balle makama.

A shekarar da ta gabata, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, wasu mutanen Amurka sun matsawa baitulmalin kasar lamba don ta rage ruwan kudin ajiyar banki, da niyyar sanya darajar kudin dala ta sauka. Sakamakon haka, a ranar 31 ga watan Yulin bana, baitulmalin tarayyar Amurka ta sanar da rage ruwan kudin ajiyar bankin kasar, wanda ya zama karo na farko da ruwan kudin ya ragu a Amurka a cikin shekaru goman da suka wuce. Game da wannan batu, wasu tsoffin shugabannin baitulmalin tarayyar Amurka hudu, ciki har da Paul Volcker, da Alan Greenspan, da Ben Bernanke, gami da Janet Yellen, sun wallafa wani sharhi a jaridar Wall Street Journal kwanakin baya, inda suka ce "Amurka na bukatar wani baitulmali mai cikakken 'yanci", kuma suka bayyana cewa kada a matsa lambar siyasa ga manufofin kudin Amurka.

Amma wasu mutanen Amurka sun yi kunnen kashi kan irin wannan kira har suke ci gaba da bukatar baitulmalin kasar ya kara karfin rage ruwan kudin ajiyar banki cikin sauri. Ana iya cewa, irin wannan matsin lambar siyasa da aka sanyawa baitulmalin Amurka shi ne wani mataki na rage darajar kudin kasar da gangan. Ita Amurka na da niyyar rage darajar kudinta, amma ta tsoma baki cikin batun raguwar darajar kudin Sin RMB, to, ku ga fuskoki biyu ne da Amurka ta nuna.

A matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, Sin ta dinga cika alkawarin da ta dauka kan batun darajar kudade a wajen tarurrukan kolin kasashen G20, ba ta taba ba, kuma ba za ta yi amfani da batun darajar kudi don tinkarar takaddamar cinikayya ba. Tun da Amurka ta kara tsananta rikicin cinikayya tsakaninta da kasar Sin a shekara ta 2018, ya zuwa yanzu, duk da cewa ita Amurkar ta rika matsawa Sin lamba, Sin ba ta taba rage darajar kudinta da gangan domin yin takara da Amurka ba, kuma a nan gaba ma ba za ta yi ba.

A wani bangaren, kasar Sin tana yin takara a kasuwannin duniya ne ba ta hanyar rage darajar kudinta RMB ba, amma ta hanyar samar da kayayyaki masu inganci kuma masu rahusa. Kasar Sin na da wani cikakken tsarin masana'antu, inda take samar da kayayyaki da dama wadanda 'yan kasuwan Amurka ke bukata sosai.

A dayan bangaren ma, zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin na cewa wai tana yunkurin rage darajar kudinta, bai dace da bukatar da Sin ke da ita ba, wato sauya salon ci gaban tattalin arzikin kasar daga ci gaba mai saurin gaske zuwa ci gaba mai inganci. A halin yanzu, tattalin arzikin kasar Sin na dogara sosai kan harkokin saye da sayarwa a cikin gida, kana, yawan gudummawar da karuwar saye da sayarwar cikin gida ta bayar ga habakar tattalin arzikin Sin ya zarce kaso 60 a farkon rabin bana, amma cinikin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje bai bayar da gudummawa sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasar ba, don haka kasar Sin ba ta bukatar rage darajar kudinta da gangan.

Hakikanin gaskiya, rage darajar kudin Sin RMB bai dace da moriyar kasar ba, kuma zargin da wasu mutanen Amurka suka yiwa kasar, ba shi da kanshin gaskiya kana kashin kaji ne da suka shafawa gwamnatin kasar Sin kawai. Abun da ba illata tattalin arzikin kasar Sin kadai zai yi ba, har ma da rage kwarjinin Amurka a idon mutanen duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China