Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana tattalin arzikin Amurka sun ce babu shaidun dake nuna cewa kasar Sin na rage darajar kudi
2019-08-08 14:36:31        cri

A kwanakin baya ne ma'aikatar kudin Amurka ta ayyana kasar Sin a matsayin wadda ta rage darajar kudinta, abun da ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar Amurka. Wasu masana tattalin arzikin Amurka na ganin cewa, babu shaidun dake nuna cewa kasar Sin na yunkurin rage darajar kudinta, kana irin abun da Amurka ta yi zai kara illata tattalin arzikin duniya baki daya.

Dajarar kudin Sin wato RMB ta ragu kan dalar Amurka a ranar 5 ga wata, wato dala daya kwatankwacin Yuan sama da 7. Daga baya ma'aikatar kudin Amurka ta sanar da ayyana kasar Sin a matsayin kasa dake rage darajar kudinta. A nasa bangaren, wani babban manazarci a cibiyar nazarin manufofin kasa da kasa ta Amurka wanda kuma shehun malami ne a jami'ar New York James Nolt ya ce, darajar kudin Sin wato RMB ta ragu saboda wasu manufofin cinikayya na bangare daya da gwamnatin Amurka ta dauka, musamman kara sanya haraji kan hajojin Sin, kana, zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin na cewa wai tana rage darajar kudinta da gangan ba shi da tushe balle makama. Malam Nolt ya ce:

"Zargin da Amurka ta yiwa kasar Sin ba shi da tushe balle makama. Gaskiyar magana ita ce, gwamnatin Amurka ta kara haifar da barazanar sanyawa kayan kasar Sin haraji, shi ne babban dalilin da ya sa darajar kudin Sin RMB ta ragu. Gwamnatin Sin ba ta taba rage darajar kudinta da gangan ba, kuma tana nuna himma da kwazo wajen daukar kwararan matakan hana darajar kudinta raguwa. Amma sakamakon matakin gwammatin Amurka na kara sanya haraji kan kayan Sin, ya sa darajar RMB ta dan ragu."

James Nolt ya bayyana cewa, darajar kudin Sin ta ragu kan dalar Amurka ne saboda karfin kasuwanni, ba don katsalandan da gwammatin kasar Sin ta yi ba. Ya ce, kamar yadda sauran manyan bankunan kasashen duniya suke yi, babban bankin kasar Sin ya tsara, gami da aiwatar da manufar kudinta daidai da nauyin dake rataye a wuyansa bisa doka, kana kuma kasar Sin ta dade tana aiwatar da manufar kudinta ta hanyar da ta dace. Nolt ya ce:

"Kamar abun da manyan bankunan sauran kasashen duniya suke yi, babban bankin kasar Sin, ya tsara gami da aiwatar da manufar kudinta ne da zummar kare darajar kudinta. Idan darajar kudi ta ragu fiye da kima, babban bankin kasa zai dauki matakan da suka dace nan take, domin hana ci gaban raguwar. Idan darajar kudin ta karu cikin saurin gaske, a nan ma babban bankin kasar zai dauki matakai don hana aukuwar lamarin. Manyan bankunan kasashen duniya dukkansu suna gudanar da irin wannan aiki, wato tabbatar da darajar kudadensu, saboda hakan na da matukar muhimmanci ga harkokin tattalin arziki da kasuwanci, gami da ci gaban tattalin arzikin wata kasa. Hakikanin gaskiya, gwamnatin kasar Sin ba ta taba daukar duk wani mataki na yunkurin ragewa, ko kuma kara darajar kudinta ba, amma ita Amurka ta kara zargin kasar Sin ba gaira ba dalili, tana mai cewa wai Sin na yunkurin rage darajar kudin ta RMB."

Malam James Nolt ya kara da cewa, har yanzu gwamnatin kasar Sin na kokarin lalibo bakin zaren daidaita rikicin dake tsakaninta da Amurka, ta hanyar farfado da shawarwari, duk da cewa Amurkar na kara daukar matakai na rashin tunani. A cewar Nolt, ainihin makasudin gwamnatin Amurka na ayyana kasar Sin a matsayin wadda ke kokarin rage darajar kudinta shi ne, matsa babbar lamba, gami da samun fifiko kan kasar Sin a yayin shawarwarinsu ta fannin tattalin arziki da kasuwanci, ta yadda Amurkar za ta kara samun moriya. Jmaes Nolt ya ce:

"Gwamnatin Amurka ta dauki wannan mataki ne saboda neman karin hujja, don kara sanyawa kayan kasar Sin haraji. Gwamnatin Amurka ma na sa ran cimma moriya ta hanyar sanya harajin, shi ya sa ta kara tada rikici, har ta yiwa kasar Sin irin wannan zargi. Gaskiyar magana ita ce, gwamnatin Amurka na neman abun fakewa, don kara sanyawa kayan Sin haraji. Har wa yau, Amurka ba ta da shirin yin fatali da yakin cinikayya, ko kuma lalibo bakin zaren daidaita takaddamar cinikayya tsakaninta da Sin, abun da take so kawai shi ne samun nasara kan kasar Sin, a yayin yakinsu na cinikayya."(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China