Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nuna fin karfin tattalin arziki ba zai samu amincewa daga al'ummun duniya ba
2019-08-07 19:36:12        cri

Kwanan baya baitul malin Amurka ya bayyana kasar Sin a matsayin "mai rage darajar kudi", sai dai ya canja nagartattun matakan da ya gindaya a kan batun, lamarin shi ma ya nuna cewa, wasu Amurkawa suna son matsa wa kasar Sin lamba kan batun darajar kudi yayin da kasar Sin take kokarin kiyaye moriyar kanta, ko shakka babu matakin zai kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya, don haka ba wanda zai amince da matakin, haka kuma ba wanda zai amfana daga matakin.

Idan an waiwayi tarihin tattalin arziki duniya, za a lura cewa, Amurka ta sha daukan irin wannan matakin domin yin takara. A shekarun 1980 zuwa 1990, Amurka ta taba ayyana Koriya ta Kudu a matsayin "mai rage darajar kudi" domin tilasta mata kara darajar kudin kasarta yayin musanyar kudinta da dalar Amurka, kana sauran kasashen duniya kamar su Jamus da Italiya da Japan da Singapore su ma sun taba shiga jerin sunayen masu rage darajar kudi da Amurka ta bayyana, a don haka ana iya cewa, domin nuna fin karfi a bangaren tattalin arziki, kullum Amurka tana daukar matakan matsa lamba, har ma ga kasashe kawayenta.

Tun bayan kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, kullum kasar Amurka na zargin wai kasar Sin ta rage darajar kudinta na RMB. A shekarar 2005, akwai 'yan majalisar tarayyar Amurka da suka gabatar da dokar kudi, inda aka yi zargin cewa, kasar Sin ta rage darajar kudinta, kana Amurka za ta kara sanya haraji don hana ta samun rangwame, da nufin tilasta mata kara darajar kudinta na RMB. Amma, tun bayan da kasar Sin ta soma yin gyare-gyare kan tsarin darajar kudin RMB a shekarar 1994, ta yadda zai yi daidai da yanayin kasuwa. A yayin shawarwarin da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi kan aya ta hudu game da kasar Sin, asusun ya nuna cewa, darajar kudin RMB ya dace da yanayin da ake ciki.

A 'yan kwanakin da suka wuce, sakamakon matakin da kasar Amurka ta dauka na gashin kai, da karfafa takaddamar cinikayya dake tsakaninta da kasar Sin, hakan ya haifar da matsala a kasuwar kudi ta duniya, kuma darajar kudin RMB na sauyawa bisa bukatun kasuwa da hasashen da aka yi, har ma wasu 'yan kasar Amurka da ba su san komai game da tattalin arziki na yau da kullum ba, da hasashen da wasu shahararrun hukumomin kasa da kasa suka yi, sun yi zargin cewa, kasar Sin ta rage darajar kudinta ne, da nufin kara matsa lamba kan kasar Sin, tare kuma da biyan bukatun cikin gidan kasar ta Amurka a fannin siyasa.

Matakin Amurka ya kawo sabon cikas ga raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, tare da haddasa mummunar matsala a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya. Game da wannan batu, tsohon ministan kudi na kasar Amurka Lawrence Summers ya yi bayani a ranar 6 ga wannan wata cewa, matakin Amurka na ayyana Sin a matsayin mai rage darajar kudi bai dace da hakikanin yanayi ba, kuma hakan ya rubar da mutuncin gwamnatin kasar Amurka, kana zai iya haddasa hadarin koma bayan tattalin arziki ga kasar Amurka.

A matsayinta na kasa mai daukar alhakinta, kasar Sin ta yi alkawarin ba za ta yi amfani da batun rage darajar kudi don tinkarar matsalar ciniki ba. Matakin Amurka na yin amfani da wannan dalili don matsawa kasar Sin lamba ba zai samu nasara ba. (Masu Fassarawa: Jamila, Bilkisu, Zainab daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China