Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Kasar Amurka ce ke da alhaki game da matsalar ciniki tsakanin Sin da Amurka
2019-08-06 11:14:09        cri

 


 

Hukumar samar da ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta Sin, da ma'aikatar cinikayyar kasar, sun ce kamfanonin kasar su dakatar da sayo kayayyakin amfanin gona daga Amurka, kana kasar na iya karawa hajojin Amurka da ake shigarwa Sin bayan ranar 3 ga watan Agusta haraji.

Wannan matakin na zuwa ne, bayan da Amurka ta ayyana karawa hajojin Sin da ake shigarwa Amurka harajin kaso 10 bisa dari, hajojin da darajar su ta kai dalar Amurka biliyan 300, matakin da Sin ke cewa ya keta hurumin matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a birnin Osaka na kasar Japan.

Don haka kasar Sin ta dauki wannan mataki don mayar da martani ga sake kara harajin kwastam da kasar Amurka ta yi. Shi wani mataki ne na dole, sam babu wani kuskure ciki. Dama kasashen Sin da Amurka suna iya biyan bukatun juna bisa hadin gwiwarsu a fannin aikin gona. Bayan da shugabannin kasashen 2 suka gana da juna a birnin Osaka na kasar Japan a karshen watan Yuni da ya gabata, kasar Sin ta fara sayen karin amfanin gona daga kasar Amurka, don biyan bukatunta na cikin gida. Tun daga lokacin har zuwa karshen watan Yuli da ya wuce, an yi jigilar wake ton miliyan 2.27 daga kasar Amurka zuwa kasar Sin. Sa'an nan a ranar 19 ga watan Yuli, wasu kamfanonin kasar Sin sun fara neman shigar da karin amfanin gona daga kasar Amurka. Zuwa daren ranar 2 ga watan Agusta, an sayi karin wake ton dubu 130, da dawa ton dubu 120, da busashen ciyayi ton dubu 75, da alkama ton dubu 60, da dai sauransu. Kuma kasar Sin bata karbi karin haraji kan wadannan kayayyakin da ake shigar da su daga Amurka ba.

Hakan ya nuna yadda kasar Sin ta dauki takamaiman matakai don aiwatar da matsayar da ta cimma tare da kasar Amurka, a lokacin ganawar shugabannin kasashen 2 a birnin Osaka. Amma a nata bangaren, kasar Amurka ta sake yin kwan-gaba kwan-baya, inda ta kara harajin kwastam kan kayayyakin kasar Sin da ake neman shigarwa kasar Amurka, lamarin da ya girgiza tushen cinikin amfanin gona da ake yi tsakanin kasashen 2. Saboda haka, ba yadda za ta yi ba sai kasar Sin ta dauki mataki kan kayayyakin amfanin gona na kasar Amurka, don kare mutunci da moriyarta. Ta wannan ma zamu iya fahimtar cewa, yadda ake matsawa kasar Sin lamba ba zai yi amfani ba, domin koda yaushe kasar zata iya mayar da martani yadda take bukata.

Kasar Sin kasa ce dake shigo da mafi yawan amfanin gona daga ketare, yayin da kasar Amurka ita ce wadda ke fitar da mafi yawan kayayyakin amfanin gona ga sauran kasashe. Saboda haka, cinikin amfanin gona ya dade yana taka muhimmiyar rawa a cinikayyar da ake yi tsakanin kasashen 2. Amma yanzu an sake haifar da tsaiko ga wannan ciniki. Game da wannan batu, kasar Amurka ce ke da cikakken alhaki.

Abin takaicin shi ne, manoman kasar Amurka dake hadin gwiwa da kasar Sin zasu sha wahala matuka sakamakon manufar kwan-gaba kwan-baya ta gwamnatin Amurka. Saboda haka, kungiyoyin manoma masu samar da wake, da masara, da alkama, da dai sauransu sun gabatar da hadaddiyar sanarwa, inda suka nuna kin amincewa ga karbar karin haraji kan kayayyakin Sin. A cewar manoman, abin da ake bukata don raya harkar noma a kasar Amurka shine habaka kasuwanni a maimakon kara haraji. A nata bangare, jaridar Los Angeles Times tace, yakin ciniki yana sanya sana'ar noma ta kasar Amurka tsunduma cikin mawuyacin hali. An yi hasashen cewa, kasar Amurka zata samu dala biliyan 69.4 bisa harkar noma a bana, adadin da ya yi kasa da kashi 45%, idan an kwatanta da na shekarar 2013, sakamakon raguwar farashin amfanin gona a kasuwannin kasa da kasa, gami da wasu bala'u daga Indallahi da ake fuskanta a kasar. Don haka, matakin karbar karin haraji da gwamnatin Amurka ta dauka a wannan karo zai zama tamkar "karawa guduma nauyi ne" ga harkar noman kasar Amurka. Dangane da batun, Gary Cohn, tsohon darektan majalisar tattalin arziki ta fadar White House, ya taba bayyana cewa, matakin karbar karin haraji ba zai gurgunta tattalin arzikin Sin kamar yadda wasu jami'an kasar Amurka ke neman samu ba, maimakon haka, zai sa harkar noma ta kasar Amurka ta fuskanci wasu manyan matsaloli.

Saboda haka, ya kamata wasu jami'ai masu kula da aikin tsara manufofi na kasar Amurka su nuna sanin ya-kamata, tare da sauraron muryar manoman kasarsu. Daga bisani zasu fahimta cewa, mataki mafi dacewa shine neman hadin gwiwa tare da kasar Sin, maimakon tada rikici tsakaninsu. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China