Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin da mashawarcin cinikin Amurka ya yi ba shi da tushe ko kadan
2019-08-05 19:24:40        cri

Jiya Lahadi 4 ga wata, mashawarci kan cinikayya na fadar White House ta Amurka Peter Navarro ya bayyana cewa, dole ne kasar Sin ta daina aikata laifuffuka bakwai, in ba haka ba gwamnatin Amurka ba za ta daina daukar matakin kara sanya haraji kan kayayyakin da za ta shigo da su Amurka daga kasar Sin ba, a sa'i daya kuma, ya kara da cewa, gwamnatin kasarsa tana gudanar da aikin share fage domin ci gaba da halartar tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da kasar Sin a watan Satumba dake tafe, to yana da wahala a gano abin da Amurka take yi yanzu, saboda an ga tana kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin da ke shiga Amurka, kana tana zargi kasar Sin kamar yadda take so, a gefe daya kuma tana son ci gaba da gudanar da tattaunawa da kasar Sin.

Laifuffuka guda bakwai da Peter Navarro ya gabatar sun shafi matakan kare 'yancin mallakar fasaha, da sayar da fasahohi, da samar da kudin rangwame ga kamfanonin mallakar gwamnati, da hana amfani da Fentanyl da sauransu, hakika zarginsa ba shi da tushe ko kadan.

Alal misali a bangaren kare 'yancin mallakar fasaha, da gaske ne gwamnatin kasar Sin tana kara mai da hankali kan wannan batu matuka, saboda tana sa kaimi kan aikin kirkire-kirkire, haka kuma sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin sun samu amincewa daga wajen al'ummomin kasashen duniya. A cikin watanni shida na farkon shekarar bana ta 2019, adadin 'yancin mallakar fasahar da 'yan kasashen waje suka nema a kasar Sin ya kai dubu 78, adadin da ya karu da kaso 8.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana adadin tambarin shaidar fasaha da 'yan kasashen waje suka nema a kasar Sin ya kai dubu 127, adadin da ya karu da kaso 15.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, duk wadannan sun shaida cewa, kasashen duniya suna amincewa da kokarin da kasar Sin take a fannin kare 'yancin mallakar fasaha.

Kwanakin baya hukumar kare 'yancin mallakar fasaha ta duniya wato WIPO ta gabatar da jerin kasashe wadanda suka fi samun ci gaba a bangaren kirkire-kirkire a shekarar 2019, inda aka bayyana cewa, kasar Sin tana matsayi na 14, ko da yake a shekarar 2018 tana matsayi na 17 ne, a don haka babban jami'in hukumar Francis Gurry ya bayyana cewa, yanzu kasar Sin tana kan gaba a tsarin kare 'yancin mallakar fasaha a fadin duniya.

Game da batun hana amfani da maganin Fentanyl, yanzu yawan nau'o'in maganin Fentanyl da kasar Sin ta hana amfani da su ya kai 25, wanda ya wuce 21 da MDD ta tanada. Tun daga ranar 1 ga watan Mayun bana, kasar Sin ta fara aiwatar da dokar hana amfani da duk wasu nau'o'in maganin Fentanyl, lamarin da ya shaida cewa, Sin na daukar dukkan nau'o'in maganin a matsayin miyagun kwayoyi, wanda ya wuce yadda Amurka ke yi kan maganin. Lamarin da ya samu jinjina daga kasashen duniya, ciki har da hukumar yaki da masu ta'ammali da miyagun kwayoyi ta Amurka.

Don haka, idan muka duba laifuffuka bakwai da Peter Navarro ya bayyana daya bayan daya, za a gano cewa, ko wanensu ba shi da tushe ko kadan, yana neman shafawa kasar Sin kashin kaza ne kawai. Dalilin da ya sa ya sake maimaita batun, shi ne sabo da yadda Amurkawa ke nuna matuka adawa da ra'ayin gwamnatin Amurka na shirya kara sanya harajin kaso 10 cikin 100 kan kayayyakin Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 300. Bangarori daban-daban na Amurka na ganin cewa, matakin zai kara kawo wa Amurka illa. Amma wasu Amurkawa kalilan ba sa martaba ra'ayin saura, suna ci gaba da neman hujja ga matakin da gwamnatin Amurka za ta dauka, a kokarin daina daukar alhakin kan matakin lalata tattalin arzikin Amurka da ita kanta ta haddasa.

Navarro ya bayyana wa wasu 'yan jaridan kafofin watsa labaru na kasar Amurka a kwanaki biyu da suka gabata cewa, masu sayayya a kasar Amurka ba za su biya karin kudin sayen kayayyaki ba idan aka kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin, amma jagoran shirin kafar watsa labaru ta CNN ya ruwaito kididdigar da kamfanin hada kujeru mai suna La-Z-Boy na kasar Amurka ya yi cewa, bayan da Amurka ta kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin a zagayen da ya gabata, kamfanin ya daga farashin kayansa da dala 42. Kana jagoran shiri na gidan telebijin na FOX ya yi nuni da cewa, rahoton da ma'aikatar cinikayya ta kasar Amurka ta gabatar, ya nuna cewa, matakan kara harajin sun haddasa karuwar farashin kayayyaki a cikin kasar Amurka.

Matakin Amurka na kara sanya haraji kan kayayyakin Sin ya haddasa matsalar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, idan bangarorin biyu suka cimma yarjejeniya, tilas ne a soke dukkan harajin kwastam da aka kara sanyawa kayayyakin Sin. Idan kasar Amurka tana son daidaita matsalar, ya kamata ta nuna adalci da girmama juna, da yin la'akari da yadda kasar Sin take kula da lamarin, da kuma sake maida hankali ga ganawar da shugabannin kasashen biyu suka yi a birnin Osaka na kasar Japan. (Jamila, Kande, Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China