Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin ranar jamhuriyar Nijer a bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa na 2019
2019-08-05 14:13:23        cri

 






A ci gaba da bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa da ke gudana a nan birnin Beijing, a jiya lahadi aka gudanar da bikin ranar jamhuriyar Nijer. Bikin dai ya samu halartar baki da dama, cikinsu har da jami'an gwamnatin kasar Sin da wasu jakadun kasashen Afrika da kuma al'ummar Sinawa da dama. Kana an gudanar da kade-kade da raye-raye na gargajiya daga wasu shahararrun mawakan jamhuriyar Nijer.

 

Jakadan Nijer a kasar Sin,Inoussa Moustapha ya halarci bikin tare da gabatar da muhimmin jawabi. A jawabin da ya gabatar, ya bayyana cewa, halartar bikin baje kolin lambunan shakatawa na kasa da kasa da Nijer ta yi a wannan karo ya shaida muhimmancin da gwamnatin kasar ta dora ta fannin raya ayyukan gona da ma kiyaye muhalli, da kuma yadda gwamnati ke mai da hankali a kan samar da isasshen abinci da ma abinci masu gina jiki ga al'ummar kasar. Ya kara da cewa, kasar Sin ta gabatar da manyan gyare-gyare ga tattalin arzikinta, kuma ta samu babban ci gaba ta fannin saukaka fatara da raya zaman al'umma, abin da ya ba kasashen Afrika matukar Kwarin gwiwa. Ya ce kasar Sin na taimakawa kasashe masu tasowa wajen saukaka fatara da kuma raya karkara, don haka, ya yi imanin hadin gwiwar kasashen biyu zai tabbatar da ci gaba mai armashi.

Wakiliyarmu Lubabatu ta hada mana wani rahoto a kan bikin.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China