Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba wanda zai more daga takarar rashin hakuri da juna
2019-08-04 20:26:33        cri

Kwanakin baya gwamnatin Amurka ta sanar da cewa, za ta kara sanya harajin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin da za ta shigo da su daga kasar Sin wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 300, matakin da ya sabawa matsayar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma yayin ganawarsu a birnin Osaka na kasar Japan. Wanda ya nuna cewa, har yanzu wasu mutanen Amurka ba su yi watsi da ra'ayin yin takara maras hakuri da juna wanda ba zai dace da yanayin da ake ciki yanzu ba, ko shakka babu lamarin ya kawo illa matuka ga tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da kasashen biyu wato Sin da Amurka suke gudanarwa, haka kuma ya lalata babbar moriyar al'ummomin sassan biyu da kuma daukacin kasashen duniya baki daya.

Ra'ayin yin takara bisa rashin hakuri da juna, yana nufin cewa, idan sassa biyu suka yi takara, tabbas ne sashe guda ya samu moriya, dayan sashen kuma ya yi hasara, ba zai yiyu sassan biyu su yi nasara tare ba. Yanzu haka wasu mutanen Amurka suna nacewa kan ra'ayin yayin da suke gudanar da harkokin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, har suna ganin cewa, karuwar tattalin arzikin sauran kasashen duniya za ta kawo illa ga tattalin arzikin Amurka, a don haka dole ne suka dauki matakan ramuwar gayya. A cikin shekara daya da ta gabata, ana iya gano irin wannan ra'ayin yin takara maras hakuri da juna daga matakan da Amurka ta dauka yayin da take gudanar da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da kasar Sin.

Amma a halin da ake ciki yanzu, daukacin kasashen duniya suna dogaro ga juna, kuma cudanyar tattalin arzikin duniya tana kara habaka cikin sauri. A bayyane yake cewa, bil Adama suna da makoma guda daya, ra'ayin yin takara bisa rashin hakuri da juna bai dace da yanayin da ake ciki ba, idan wasu mutanen Amurka wadanda ke nacewa kan ra'ayin suna son neman samun ci gabanta wato kasa daya kadai, hakan ba zai yiyu ba ko kadan, saboda ra'ayin ya sabawa ka'idar ci gaban tattalin arziki, da ka'idar ci gaban tarihi, ba wanda zai more daga ra'ayin.

A don haka, bangarori daban daban dake cikin kasar Amurka sun nuna adawa ga matakin da gwamnatin kasar ta dauka, wato kara sanya harajin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin da za ta shiga da su daga kasar Sin wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 300, inda kungiyoyin sana'o'i da kafofin watsa labarai na Amurka suka yi nuni da cewa, matakin zai lalata moriyar masu sayayya na kasarsu kai tsaye, kila zai sa wasu kantunan kasar su rufe kofa, ko kuma zai sa wasu Amurkawa da dama su rasa guraben aikin yi.

A sakamakon tsananta rikicin ciniki, bankin duniya ya gabatar da rahoto na hasashen tattalin arzikin duniya a watan Yuni, inda ya rage hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya na bana daga kashi 2.9 cikin dari zuwa kashi 2.6 cikin dari. Idan kasar Amurka ta dauki sabbin matakan kara buga harajin kwastam ga kasar Sin, matakin zai sabawa ka'idojin hukumar ciniki ta duniya, da kawo illa ga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban da kuma tsarin samar da kayayyaki na duniya. Hakan zai kara kawo illa ga tattalin arzikin duniya, da sa kaimi ga samun koma baya ga tattalin arzikin duniya.

A matsayin manyan kasashe biyu mafiya samun bunkasuwar tattalin arziki a duniya, Sin da Amurka na da matsalolin tattalin arziki da cinikayya da dama, ya kamata a warware su ta hanyar yin shawarwari cikin sahihanci.

Ya kamata wasu mutanen kasar Amurka su gano hakikanin yanayin da ake ciki a yanzu, da bin tsarin bunkasuwar tattalin arziki, da yin watsi da ra'ayin yin takara a tsakanin kasa da kasa wadanda yawan ribar da suka samu ta yi daidai da yawan hasarar da sauran kasashe suka tabka, da yin kokarin samar da yanayi mai kyau na yin shawarwari don daidaita matsalolinsu.

Sin ta maida shawarwari a matsayin zabi mafi dacewa wajen daidaita matsalolin tattalin arziki a tsakaninta da kasar Amurka. Amma Sin ta tsaya tsayin daka kan kiyaye moriyar kasa da ta jama'arta. Idan za a yi shawarwari, to za ta maraba da shi. Idan kuma aka tada rikici, za ta mayar da martani. (Jamila, Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China