Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Idan ba a cika alkawari ba, ba za a samu nasara wajen yin shawarwari ba
2019-08-03 20:09:37        cri
Kwanan nan, kasar Amurka ta kara daukar matakin sanya haraji, ta yi shirin kara karbar haraji da kaso 10 cikin 100 kan kayayyaki masu darajar dala biliyan 300 da zata shigo dasu daga kasar Sin a ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa, a waje guda kuma, ta ce tana fatan yin shawarwari mai yakini tare da kasar Sin da nufin cimma wata yarjejeniyar cinikayya da kasuwanci a dukkan fannoni. A yayin da take sabawa alkawarin da ta dauka da ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma a Osaka na kasar Japan, a sa'i daya kuma tana fatan cimma sakamako mai kyau a yayin shawarwari, gaskiya ba za'a iya fahimtar dabarar tunaninta ba. Nuna gaskiya da cika alkawari su ne tushen yin shawarwari, a matsayinta na wata kasar da kullum ke yin amai ta lashe, ta yaya za ta iya samun amincewa daga wajen kasar Sin?

A cikin shekara sama da daya da ta wuce, ko da yaushe kasar Sin na nuna sahihanci wajen yin shawarwari tare da Amurka. Amma, a kan gamu da matsaloli ne sakamakon sabawa ra'ayin bai daya da kasar Amurka ta yi har sau hudu.

A watan Fabrairun shekarar 2018, kasashen Sin da Amurka sun cimma ra'ayin bai daya bisa matakin farko kan batutuwan da suka shafi kara shigo da amfanin gona daga wajen kasar Amurka, da kayayyakin makamashi da dai sauransu. Amma, a watan Maris na shekarar, kasar Amurka ta bayar da rahoton bincike kan kasar Sin, inda ta sanar da cewa, zata kara karbar haraji da kaso 25 cikin 100 kan kayayyaki masu darajar dala biliyan 50 da take shigowa daga wajen kasar Sin.

Sa'an nan, Sin da Amurka sun fitar da wata sanarwar hadin-gwiwa a ranar 19 ga watan Mayun shekarar 2018, inda suka cimma matsaya kan dakatar da yin yakin cinikayya tsakaninsu. Amma bayan kwanaki goma kacal, fadar White House ta yi fatali da sanarwar har ta sanar da ci gaba da aiwatar da shirin kara sanyawa hajjojin Sin haraji.

Daga baya wato ranar 1 ga watan Disambar shekara ta 2018, shugabannin kasashen biyu sun cimma matsaya a yayin da suke ganawa da juna a kasar Argentina, inda suka amince da dakatar da sanyawa kayan juna sabon haraji, da gaggauta yin shawarwari cikin kwanaki casa'in, a wani kokari na soke dukkan harajin da aka kara sanyawa. Amma ita Amurka ta kara gindaya sharruda a wajen shawarwarin, har ma a ranar 10 ga watan Mayun bana, ta kara sanya harajin kaso 25 daga kaso 10 kan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa Amurka da darajarsu ta kai dala biliyan 200, al'amarin da ya kawo babban cikas ga shawarwarin kasashen biyu.

Zuwa ranar 29 ga watan Yunin bana, shugabannin Sin da Amurka sun sake cimma matsaya a birnin Osakan kasar Japan, inda suka yarda da sake farfado da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya bisa tushen nuna adalci da girmama juna, kana Amurka ba zata sake sanya sabon haraji kan kayayyakin da Sin ke shigarwa kasar ba.

Daga bisani bangarorin Sin da Amurka sun gudanar da shawarwari tsakanin manyan jami'ansu dangane da batun tattalin arziki da cinikayya a karo na 12, inda suka yarda da sake gudanar da shawarwari a kasar Amurka a watan Satumba mai zuwa. Sai dai wasu sa'o'i 30 kawai bayan kammala shawarwarin na wannan karo, kasar Amurka ta sake nuna kwan-gaba kwan-baya, ta jefa shawarwarin da ake yi cikin wani mawuyacin hali.

Ta wadannan batutuwa za a iya ganin cewa, kasar Amurka ce ke da cikakken alhaki game da matsalolin da ake fuskanta a shawarwarin da ake yi tsakanin Sin da Amurka kan batun tattalin arziki da cinikayya. Kowa ya sani, aikin shawarwari ya kan shafi bangarori 2. Idan ana son cimma matsaya, to, dole bangarorin 2 su nuna hakuri da sahihanci. Yanzu kusan shekara daya bayan kaddamar da shawarwari tsakanin Sin da Amurka, kasar Sin tana ta kokarin cika alkawarin da ta yi, da aiwatar da matakan da aka cimma matsaya a kai. Amma a nata bangaren, kasar Amurka ta kan yi amai ta lashe, sam bata da gaskiya. Lamarin da ya haddasa matsaloli ga aikin shawarwari, gami da baiwa al'ummun duniya mamaki.

Har kullum kasar Sin na dauke da ra'ayin cewa, matakin karbar karin harajin kwastam ba zai taimakawa daidaita matsalolin da ake fuskanta tsakanin kasashen Sin da Amurka ba. Za a samu warware matsalar ne ta hanyar shawarwari kawai. Duk da haka, kasar Sin bata tsoron duk wani matakin matsin lamba, kuma a shirye take wajen tinkarar duk wani kabubale. Idan wasu jami'an kasar Amurka za su ci gaba da kwan-gaba kwan-baya, to, koma dai wane irin kokarin shawarwari ake yi, ba zai haifar da da mai ido ba. (Bilkisu, Murtala, Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China