Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsa babbar lamba ba zai taimaka ga warware matsala ba
2019-08-02 19:44:23        cri
Bayan da aka kammala shawarwarin tattalin arziki da kasuwanci zagaye na 12, tsakanin manyan jami'an gwamnatocin Sin da Amurka bada jimawa ba, Amurka ta sake yin barazanar cewa, za ta kara sanya harajin kaso 10 kan hajjojin da aka rage, wadanda kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka da darajarsu ta kai kimanin dala biliyan dari 3, al'amarin da a cewar kasar Sin, ya sabawa matsayar da shugabannin Sin da Amurka suka cimma, a yayin ganawar da suka yi kwanakin baya a birnin Osakar kasar Japan, wanda ba zai kai ga warware matsala ba.

Kasar Sin na nuna matukar rashin jin dadi, da kin amincewa da wannan kuduri na Amurka, kana za ta dauki duk wani matakin da ya wajaba domin kare babbar moriyar ta, gami da al'ummarta baki daya.

A shekarar da ta gabata, lokacin da bangaren Amurka ke shawarwari tare da kasar Sin, ta kan dauki matakan matsawa Sin babbar lamba. Amma shaidu sun nuna cewa, wadannan matakai ba su da amfani sam, wadanda ba kawai za su lalata damammakin sake farfado da shawarwari tsakanin kasashen biyu ba, har ma ba za su taimaka ga daidaita matsaloli da kawar da sabani ba.

Yayin shawarwarin tattalin arziki da kasuwanci zagaye na 12 da aka gudanar tsakanin manyan jami'an gwamnatocin Sin da Amurka, sun kasance karo na farko da tawagogin kasashen biyu suka gana da juna, tun bayan da aka katse shawarwarinsu sama da wata biyu. Kasashen biyu sun fitar da sanarwarsu bayan shawarwarin, inda suka amince cewa za su kaddamar da sabon zagayen shawarwari a watan Satumbar bana, kana tawagoginsu za su kara ganawa da juna a watan Agusta. Cimma irin wadannan nasarori ba shi da sauki, kana kuma kasashen duniya na fatan Sin da Amurka za su ci gaba da zurfafa shawarwari bisa tushen adalci da girmama juna, gami da ra'ayi daya da shugabanninsu suka cimma a Japan.

Amma, matakin da kasar Amurka ta kara dauka na kara sanya haraji, ya saba wa hanyar da ta dace wajen warware matsaloli ne a tsakanin kasashen biyu. Kullum kasar Sin na kokarin cika alkawarin da ta dauka, wajen cimma ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a birnin Osaka na kasar Japan, don haka, zargin da Amurka ta yi kan cewa wai kasar Sin ba ta samu ci gaba kan kara shigo da kayayyakin aikin gona daga Amurka, da kayyade kayayyakin Fentanyl ba ya da tushe ko kadan.

Tun daga ranar 19 ga watan Yulin bana, wasu kamfanonin kasar Sin sun riga sun soma neman farashin wasu nau'o'in amfanin gona daga 'yan kasuwar Amurka, ciki har da wake, da auduga, da dawa da sauransu. Bisa bukatun cikin gida da ka'idojin kasuwa kuma, wasunsu sun riga sun sayi wasu amfanin gonar daga 'yan kasuwar Amurka. Yanzu kuma, wasu kamfanonin sun fara tambaya ga hukumomin da batun ya shafa na kasar Sin, don neman dakatar da karbar haraji kan wadannan amfanin gona dake shigowa daga Amurka, kuma ana gudanar da aikin bincike ne bisa tsari yadda ya kamata. Saboda haka, ya kamata kasar Amurka ta yi la'akari sosai kan lokutan da ake bukata wajen gudanar da wannan aiki, kada ta yi gaggawa sosai.

Game da batun kayyade kayayyakin Fentanyl, akwai bukatar a yi hadin kai na wani tsawon lokaci a tsakanin kasa da kasa wajen warware matsalar. Hukumomin amfani da dokokin kasar Sin, sun taba tono wasu laifuffukan gyara da sayar da kayayyakin Fentanyl zuwa Amurka ba bisa doka ba, inda aka gano cewa, an gudanar da laifuffukan ne sakamakon hadin kai a tsakanin masu aikata laifuka na cikin gida da na waje, wadanda ke shafar kayayyaki kadan, wanda ba zai yiwu ba kasar Sin ta kasance muhimmin asali na yaduwar kayayyakin Fentanyl a kasar Amurka.

Abubuwan da suka faru a shekarar da ta gabata sun shaida cewa, babu wanda zai ci nasarar yakin cinikayya, kuma sanya haraji ba zai taimaka ga daidaita batun da ke jawo hankalin Amurka ba, a maimakon haka, zai lalata moriyar kasashen biyu, da ma sauran sassan duniya baki daya.

Rahoton da masanan asusun ba da lamuni na duniya IMF suka bayar a watan Mayun da ya wuce ya nuna cewa, 'yan kasuwar Amurka, da ma masu sayayya na kasar kusan sun biya dukkanin asarori a sanadin harajin da gwamnatin kasar ta sanya.

Duk da cewa tabarbarewar takaddamar ciniki ta kara matsa wa tattalin arzikin kasar Sin, amma tattalin arzikin kasar ya gudana yadda ya kamata a farkon rabin shekarar bana, in an yi la'akari da muhimman ma'aunan tattalin arziki, abin da ya shaida ingancin tattalin arzikin kasar Sin. A sa'i daya kuma, yawan kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa Amurka ya ragu da kaso 2.6% a kwatankwacin makamancin lokacin bara, a yayin da yawan kayayyakin da ta shigo da su daga Amurka din ya ragu da kaso 25.7%, alkaluman da suka nuna cewa, kasar Sin na iya shigowa da kayayyaki daga sauran kasashen duniya, don su maye gurbin kayayyakin Amurka.

A sabili da haka, yadda wasu 'yan Amurka suke ta maganar kara sanya haraji a kan kayayyakin kasar Sin da suka kai dala biliyan 300, ba zai tsorata al'ummar Sinawa ba. Sinawa na da karfin tinkarar yakin ciniki da Amurka ta tada. Idan da gaske ne Amurka ta kara sanya haraji a kan kayayyakin kasar Sin, lalle ba yadda za ta yi, sai ita ma kasar Sin ta dauki matakan da suka wajaba, don kare hakkinta. (Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China