Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda yarjejeniyar INF ta daina aiki zai tsananta barazanar da duniya ke fuskanta ta fannin tsaro
2019-08-02 17:00:25        cri

A yau Jumma'a yarjejeniyar kawar da makamai masu linzami masu cin gajere da matsakaicin zango, wato yarjejeniyar INF a takaice a tsakanin Amurka da Rasha ta daina aiki a hukunce bayan cika watanni shida da Amurka ta yi shelar janyewa daga yarjejeniyar, yarjejeniyar tana da muhimmiyar ma'ana a fannin kiyaye tsaron duniya. Yadda Amurka ta kare aniyarta ta janyewa daga yarjejeniyar wani mataki ne da kasar ta dauka don kiyaye ra'ayinta na kashin kai da kuma babakeren da ta ke yi a duniya, wanda kuma babu shakka zai raunana amincewa da juna a tsakanin manyan kasashe tare da kara takarar kera makamai a tsakaninsu, wanda hakan zai haifar da sabuwar barazana ga halin da duniya ke ciki.

An daddale yarjejeniyar INF tsakanin tsohuwar tarayyar Soviet da kasar Amurka a shekara ta 1987, inda yarjejeniyar ta tanadi cewa, kasashen biyu ba za su ci gaba da mallaka ko kera ko kuma gwajin makami mai linzami dake cin zangon da ya kai kilomita 500 zuwa 5500 da na'urorin harba shi ba. Yarjejeniyar ta kasance irinta ta takaita yaduwar makamai mafi muhimmici a lokacin yakin cacar baka, wadda ta taka rawar a-zo-a-gani a fannin rage zaman doya da manya tsakanin Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet da hana yaduwar makaman nukiliya.

Tun lokacin da gwamnatin Donald Trump ta kama aiki, ya zuwa yanzu, ta dinga daidaita manufofin tsaro yayin da take mu'amala da sauran kasashe, kuma ana kara samun sabani tsakanin Amurka da Rasha wajen aiwatar da yarjejeniyar ta INF.

Ran 1 ga watan Fabrairun bana, sakataren harkokin waje na kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, Amurka za ta daina martaba kunshin yarjejeniya, tare da shirin janyewa cikin watanni shida. Don mayar da martani kan matakin na Amurka, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sa sannu kan wani umurni a watan Maris a bana na daina martaba yarjejeniyar.

A hakika, Amurka ta fake da batun barazanar tsaro daga waje don janyewa daga yarjejeniya a kashin kanta, da nufin yin biris da tsarin tsaro na kasa da kasa ta yadda za ta kyautata da kuma kara karfin girka soji, matakin da ya bayyana tunaninta na babakere don biyan bukatunta na tsorantar da sauran kasashe da karfin soja.

Matakin janyewa daga yarjejeniyar INF da Amurka ta dauka, zai lalata yanayin tsaro da duniya ke ciki. Da farko, zai kara tsananta huldar dake tsakanin kasashen Amurka da Rasha. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta lalace sosai sakamakon zargin da aka yiwa tawagar yakin neman zaben shugaba Trump game da yin mu'amala da bangaren Rasha, da kuma ricikin da aka tayar a tsakanin Rasha da Ukraine da dai sauransu. Mataimakin ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergey Ryabkov ya yi gargadi a kwanan baya cewa, idan kasar Amurka ta jibge makamai masu linzami da yarjejeniyar ta hana a wuraren dake da kusa da kasarsa, to akwai yiwuwa kasar Rasha ita ma za ta jibge makamai masu linzami a kusa da Amurka. Na biyu, a matsayinsa na muhimmin yankin da kasashen Amurka da Rasha ke yin takara, Turai zai fuskanci babban hadari a fannin tsaro.

Yanzu kasar Amurka ta jibge wasu na'urorin harbo makamai masu linzami na kasar Rasha a wasu kasashen dake gabashin nahiyar Turai, don haka kasar Rasha za ta dauki mataki don tinkarar wannan yanayi. Hakan wata alama ce ta tsanantar yanayin adawa da juna tsakanin kasar Rasha da kungiyar tsaro ta NATO. Sa'an nan na 3, yanayin tsaro a yankin Asiya da tekun Pasific baki daya, zai zama mai sarkakiya matuka. Idan kasar Amurka ta jigbe karin makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango a wannan yanki, to, lamarin zai haddasa gasar mallakar karin makamai a yankin.

Bayan da kasar Amurka ta sanar da dakatar da martaba yarjejeniyar kau da makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango bisa kashin kanta, kasar Sin tana kokarin neman ganin kasashen Amurka da Rasha za su yi shawarwari don kare yarjejeniyar maimakon lalata ta. Sanin kowa ne cewa, kasar Amurka ita ce ta mallaki mafi yawan makaman nukiliya a duniya, saboda haka ya kamata kasar, ta fara sauke nauyin dake bisa wuyanta na rage wadannan makaman.

Kamata ya yi Amurka ta aiwatar da yarjejeniyar da ta riga ta rattaba hannu a kai, ta kuma kara rage yawan makaman nukiliya da ta mallaka, a kokarin samar da sharadi don ganin sauran kasashe sun shiga shawarwari kan rage yawan makaman, a maimakon kin sauke nauyi dake wuyanta, ta kuma dora laifin kan wasu.

Janyewar Amurka daga yarjejeniyar INF ta haifar da karuwar barazanar tsaro a duniya, lamarin dake kara nuna cewa, Amurka tana bin ra'ayin nuna bangaranci, ta kuma tada takara a tsakanin manyan kasashe, kana ta bar takarar ta yi kamari. Har ila yau shaidu sun sake tabbatar da mana cewa, ba za a iya tabbatar da tsaron lafiyar 'yan Adam ba, sai an hada kai a maimakon yin fito-na-fito, a kuma nemi amfanawa kowa a maimakon yin danniya. (Lubabatu, Murtala, Amina, Bilki, Bello, Tasallah)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China