Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Uganda: ci gaban kasar Sin ya sa masa kaimi sosai
2019-08-02 14:53:36        cri

A bana ake murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. A cikin shekarun 70 da suka wuce, 'yan siyasan kasashe da dama sun kulla hulda da dangantaka da kasar Sin, wadanda kuma suka ganewa idanunsu ci gaban da kasar Sin ta samu. Shugaban kasar Uganda Yoweri Kaguta Museveni, daya ne daga cikin irin wadannan 'yan siyasa. Ya sha kawo ziyara kasar Sin sau da dama, ya kuma jinjina wa hanyar da kasar Sin ke bi wajen raya kasa sosai. A kwanakin baya, ya zanta da wakiliyarmu.

A cikin fadar shugaban kasa da ke yankin Mbarara a yammacin kasar Uganda, shugaba Museveni ya bayyana wa wakiliyarmu labarun da ke tsakaninsa da kasar Sin. A cewarsa, nasarar da kasar Sin ta samu wajen yin juyin juya hali a kasar, ta karfafa gwiwar kasashen Afirka da kuma taimaka musu wajen yin gwagwarmaya da tsarin mulkin mallaka. "Tun bayan shekarar 1949 har zuwa yanzu, kasar Sin tana bin manufar diplomasiyya ta cin gashin kai da daidaici, lamarin da ba ita kanta kadai ya amfanawa ba, har ma da taimaka wa kasashen Afirka. Mun samu goyon baya yayin da muke yaki da 'yan mulkin mallaka. A karkashin shugabancin marigayi Mao Zedong, kasar Sin ta samu babban ci gaba, tare da samun makaman nukiliya a shekarar 1965."

Tun bayan shekarun 1980, shugaba Museveni ya kawo wa kasar Sin ziyara sau da dama, inda ya ga manyan sauye-sauyen da kasar Sin ta samu da idonsa. Ya bayyana cewa, a cikin hotunan da aka dauka a shekarun 1960, akwai kekuna da yawa a birnin Beijing. Amma yanzu motoci sun samu rinjaye a titunan kasar ta Sin. Manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare da kasar Sin take aiwatarwa ta kaddamar da aikin zamanintar da wannan kasa. "Marigayi Deng Xiaoping ya jagoranci yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen ketare. Kasar Sin ta kuma samu babban ci gaba ta fuskar masana'antu da manyan ababen more rayuwar jama'a. Yanzu kasar Sin ta zama kasa mai karfin tattalin arziki ta biyu a duniya. Dukkansu nasarori ne da Sin ta samu sakamakon yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje."

A shekarar 1986, Museveni ya hau mukamin shugaban Uganda kuma ministan tsaron kasar da babban kwamandan rundunar kasar. Bayan da ya fara mulkin kasarsa, yana bin manufofin sulhunta al'umma da bude kofa ga kowa a harkokin siyasa. Sakamakon hakan Uganda ta fitar da kanta daga yake-yake na tsawon shekaru, ta fara samun ci gaban tattalin arziki. Museveni ya ce, ci gaban kasar Sin ta sa masa kaimi sosai.

A watan Yunin bana, shugaban Museveni ya sake ziyararta kasar Sin, inda ya yi shawarwari da shugaban kasar Sin Xi Jinping. Shugabannin 2 sun amince da daga huldar da ke tsakanin kasashen 2 zuwa huldar abota da yin hadin gwiwa daga dukkan fannoni.

Yanzu kamfanonin kasar Sin da yawa suna ta zuwa Uganda zuba jari, musamman ma kan manyan ababen more rayuwar jama'a. Sin da Uganda suna hada kansu a fannoni da dama. Dangane da makomar huldar da ke tsakanin Sin da Uganda, Museveni ya yi fatan kara inganta hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin ciniki, zuba jari da aikin yawon bude ido. "Muna sayen kayayyaki da yawa daga kasar Sin, yayin da muke fatan kasar Sin za ta sayi kayayyaki da yawa daga kasarmu. Sa'an nan kasar Sin na zuba jari a kasashen Afirka. Muna fatan za mu iya zuba jari a kasar Sin. Har ma da fannonin yawon shakatawa."

A shekarun baya, sakamakon saurin bunkasuwar cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ya haifar da karuwar jita-jita da soke-soke. Dangane da tarkon bashi da ake zargin kasar Sin ta danawa kasashen Afirka, shugaba Museveni ya yi nuni da cewa, kalaman, karya ne kawai. "Ina son in tambayi wadanda suke ganin cewa, wai jarin da kasar Sin take zubawa Afirka ya kawo wa nahiyar illa. Don me suka yi irin wadanan kalamai? Lantarki, harsashi ne wajen raya tattalin arziki da masana'antu. Kasar Sin tana taimaka mana wajen samar da isasshen wutar lantarki. Don me ba za mu iya yin maraba da hakan ba? Ko ba a so Afirka ta samu ci gaba? Kana kuma, sufuri, musamman ma layin dogo, tushe ne wajen zamanintar da tattalin arzikin kasa. Kasar Sin ta fi zuba jari a kan layin dogo a Afirka. Me ya sa wasu ba su ji dadin ganin hakan ba? Ashe, ba sa so a kara azama kan ci gaban Afirka." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China