Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya Dace A Kara Yin Shawarwari Tsakanin Sin Da Amurka Bisa Adalci Da Girmama Juna
2019-08-01 14:38:24        cri


An kammala shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka zagaye na 12 jiya a birnin Shanghai na kasar Sin. A yayin shawarwari na kwanaki biyu, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan manyan batutuwan tattalin arziki da cinikayya bisa matsayar da aka cimma a yayin ganawar shugabannin kasashen biyu a birnin Osaka na kasar Japan. Kana bangarorin biyu sun tattauna kan yadda Sin za ta sayi kayayyakin amfanin gona na kasar Amurka bisa bukatunta, da kuma yadda Amurka za ta samar da kyakkyawan yanayi a wannan fanni. Bangarorin biyu sun tsai da yin sabon zagayen shawarwari a watan Satumba mai zuwa a kasar Amurka.

Abu ne mai wuya ga bangarorin Sin da Amurka da suka cimma irin wannan sakamako. Daga watan Fabrairu na shekarar 2018 zuwa yanzu, bangarorin biyu sun tattauna sau 12, wadanda suka samu babban ci gaba amma tare da fuskantar kalubale. Musamman tun daga ranar 10 ga watan Mayu, kasar Amurka ta kara sanya haraji kan kayayyakin da Sin take fitarwa zuwa kasar Amurka da darajarsu ta kai dala biliyan 200, wanda ya sabawa daidaiton da bangarorin biyu suka cimma ta hanyar yin shawarwari, da kawo illa ga yin shawarwari a tsakaninsu, har ma ga tattalin arzikin duniya baki daya. Asusun bada lamuni na duniya wato IMF ta gabatar da sabon rahoto game da makomar tattalin arzikin duniya a kwanakin baya, inda yake hasashen cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 3.2 cikin dari a bana, sai kuma kashi 3.5 cikin dari a badi, wanda ya ragu da kashi 0.1 cikin dari bisa hasashen da aka yi a watan Afrilu.

Sanin kowa ne cewa, babu wanda zai ci nasara a rikicin ciniki, hadin gwiwa ita ce hanya mafi dacewa ga Sin da Amurka. A yayin ganawar shugabannin kasashen biyu a birnin Osaka na kasar Japan a karshen watan Yuni, sun amince da sake yin shawarwari kan batutuwan tattalin arziki da cinikayya bisa tushen adalci da girmama juna, da kokarin daidaita matsalolin da suke fuskanta kamar yadda ya kamata. Don haka, wannan zagaye na 12 na shawarwarin na da babbar ma'ana ga sassan biyu, shawarwarin na zuwa ne bayan dakatar da shi har na tsawon fiye da watanni 2, kana kasa da kasa suna fatan Sin da Amurka za su warware matsalolin dake kasancewa tsakaninsu ta hanyar yin shawarwarin.

Bisa sakamakon da aka samu a gun shawarwarin, bangarorin biyu ba su yi watsi da matsalarsu ba, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan manyan batutuwan da suke mayar da hankali a kansu, wannan ya shaida cewa, suna son daidaita matsalarsu yadda ya kamata.

Hakazalika, bangarorin biyu sun tattauna batun sayen kayayyakin amfanin gona, wato Sin za ta kara sayen kayayyakin amfanin gona na kasar Amurka bisa bukatunta, a hannu guda kuma, kasar Amurka za ta samar da kyakkyawan yanayi a wannan fanni. Lamarin ya shaida cewa, bangarorin biyu suna da burin aiwatar da ayyukan da shugabannin biyu suka cimma daidaito a yayin ganawarsu a birnin Osaka ta hanyar yin hadin gwiwa.

A yayin shawarwarin, bangarorin biyu sun amince za su sake yin shawarwari a watan Satumba na bana a kasar Amurka. Rahotanni na cewa, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashen biyu, za su sha yin tattaunawa a watan Agusta kafin ganawar da za su sake yi a kasar Amurka. Wannan ya shaida cewa, bangarorin biyu dukkansu suna da niyyar kara yin shawarwari, ta yadda za su iya daidaita matsalolin dake kasancewa tsakaninsu kamar yadda ake fata.

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana kokarin martaba matakan yin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya a tsakaninta da kasar Amurka. Yin shawarwari, ita ce hanyar da ake bukata wajen daidaita matsaloli da rikicin dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Don haka, ya kamata su yi hadin gwiwa da shawarwari bisa ka'idoji, kana Sin tana adawa da duk wani abin da ya sabawa ka'idoji da moriyarta. A cikin shekara daya ko fiye, kasashen duniya sun fahimci cewa, Sin tana da karfin tinkarar rikicin ciniki a wannan karo. Kuma kasar Sin, za ta yi kokarin gudanar da harkokinta yadda ya kamata, da tsayawa tsayin daka kan manufofinta na yin kwaskwarima da fadada bude kofa ga kasashen waje. Haka kuma kasar Sin tana kokarin tabbatar da zaman lafiya a duniya, da samar da gudummawa wajen samun ci gaba, da tabbatar da odar kasa da kasa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China