Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara matsawa kasar Sin lamba ba zai dakile ta cikin shawarwarin Sin da Amurka ba
2019-07-31 15:13:16        cri

An yi tattaunawa tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka karo na 12 a jiya Talata a birnin Shanghai. A daidai wannan lokaci kuma, bangaren Amurka ta fitar da labari cewa, wai manufar kara bugawa kasar Sin haraji ta tsorantar da kasar Sin, kuma Amurka tana cin gajiyar hakan, har ta zargin kasar Sin ba gaira ba dalili na cewa, a karshe dai Sin ta gyara abubuwan dake cikin yarjejeniyar da suka samu a taro bisa moriyar kanta. Wasu Amurkawa ba su bayyana sahihanci na gudanar da shawarwarin ba, duk da ganin wahalhallu masu dimbin yawa da suka shanye wajen farfado da shawarwarin, matakin da ya teka matsaya daya da aka samu a taron Osaka, duk abin da suke so shi ne neman cin zarafi kan kasar Sin cikin shawarwari bisa yunkurin kara matsawa kasar Sin lamba.

A cikin shekara daya da ta gabata, Sin da Amurka sun kai ga matsaya daya kan yawancin batutuwa bayan shawarwari fiye da sau 10 tsakaninsu, duk da ganin mawuyancin hali da aka ciki, saboda a kullum Amurka ta kan matsa tsananin lamba kan kasar Sin don cimma burinsu, matakin da ya kawo cikas ga ikon mulki da mutuncin kasar Sin, hakan ya sa bangarorin biyu ba su iya daidaita bambancin ra'ayinsu cikin dogon lokaci. An ce, a karshen watan Yuni, shugabannin bangarorin biyu sun kai ga matsaya daya a ganawar tasu a Osaka, inda suka amince da farfado da shawarwari bisa adalci da mutunta juna, ta yadda za a daidaita batu tsakaninsu yadda ya kamata.

An iya ganin cewa, baya-bayan nan jiragen ruwa daukar wake mai nauyin fiye da ton miliyan sun tashi daga Amurka zuwa kasar Sin, sa'i daya kuma, Amurka ta sanar da soke harajin da ta bugawa kayayyaki nau'o'i 110 shigar Amurka daga kasar Sin, tare da bayyana fatanta na sa kaimi ga kamfanoninta da su ci gaba da samarwa kamfanonin kasar Sin kayayyakin da suke bukata. Matakin da ya bayyana sahihancin bangarorin biyu na tabbatar da matsaya daya da suka cimma a Osaka, saboda hakan bangarori daban-daban na sa ran an samun sakamako mai kyau cikin shawarwarin Sin da Amurka karo na 12.

Amma, Amurka ta sake yin makirci na matsa lamba, matakin da ba zai kawo illa ga kasar Sin ba a da, balle a yau har nan gaba, har ta gaji da ganin hakan. Shekara daya da ta gabata, Amurka ba ta ci gajiyar takaddamar cinikin da ta tayar ba, kuma Sin ba ta ci tura ba, duk da cewa tana fuskantar kalubalen koma bayan tattalin arzikinta a farkon rabin shekarar bara, amma tattalin arizkinta na samun bunkasuwa ba tare da wata tangarda ba, alkaluman wasu nau'o'in tattalin arziki na tafiyar yadda ya kamata, matakin da ya bayyana matukar karfi da kuzari da kuma makomar tattalin arzikin Sin mai kyau.

A maimakon haka, GDPn watannin Afrilu, Mayu da Yuni ya ragu zuwa kashi 2.1 cikin dari, wanda ya kasa samun saurin bunkasuwa bisa na kashi 3.1 cikin dari na watannin Jarairu, Fabrairu a Maris na bana. Sana'ar samar da kayayyaki na fama da mawuyancin hali, bisa kididdigar da bankin St. Louis ya bayar an ce, yawan kayayyakin da Amurka ta samar ya rika ragu a farkon rabin shakarar bana. Ban da wannan kuma, kungiyar IMF ta gabatar da sabunta rahoton hangen nesa kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya, inda an yi kiyasin cewa, yawan bunkasuwar tattalin arzikin Amurka zai kai kashi 2.9 cikin dari, wannan alkaluma za ta ragu zuwa kashi 1.9 cikin dari a badi. Saboda ganin hakan, fadar shugaban Amurka ta yi kira ga babban bankin Amurka sau da dama da ta rage kudin ruwansa da kaso mai yawa. Wasu Amurkawa sun jirkita abin gaskiya har sun shafawa kasar Sin kashin kaji da nufin matsawa kasar Sin lamba, da kuma boye hakikanin halin da kasar ke ciki na koma bayan tattalin arizkinta.

Amurka ta zargi cewa, wai Sin ta gyara yarjejeniyar da suka samu ba ta da wata hujja ba, hakika dai tana neman dora hakkin kan kasar Sin game da mawuyacin halin da aka fuskanta cikin shawarwari. Ya zuwa yanzu, bangarorin biyu ba su kai ga wata yarjejeniya ba tukuna, an yi gyarawa kan wasu batutuwa da aka rubuta cikin takardu da abubuwan da aka fadawa, kullum ne aka yi cikin shawarwari, Amurka ma ta kan yi haka a cikin shawarwari fiye da 10 da suka gabata, don me ta zargin kasar Sin game da wannnan batu? A hakika dai, Amurka ta sabawa matsaya daya da bangarorin biyu suka cimma, da keta abin gaskiya da rashin bayyana sahihanci, kana da ta yi amai ta lashe, mataki ne da suka kawo cikas ga shawarwarin bangarorin biyu.

Amurka ta tayar da takaddamar ciniki tsakaninta da kasar Sin har tsawo shekara daya da wani abu, a karshe dai an koma teburin shawarwari bayan iyakacin kokarin da suka yi. Muhimmin abu dake gabansu wajen samun ci gaba mai kyau shi ne, tabbatar da matsya daya da suka samu a Osaka, wato ta yi watsi da yunkurin matsawa kasar Sin lamba da nacewa ga adalci da mutunta juna da kula da batutuwan dake shafi murdun bangarorin biyu. Ban da wannan kuma, a maimakon matakin da wasu Amurkawa suka dauka na kawo cikas ga shawarwari, ya kamata sun sa kaimi ga samun wata yarjejeniya mai adalci da cin moriya tare. Amurka za ta dandana kudarsu idan ta ci gaba da makircinta. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China