Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Cutar ana azabta mana" da Michael Pillsbury ya kamu da ita ta tsananta
2019-07-28 21:17:37        cri

A kwanan baya, Michael Pillsbury na kasar Amurka, wanda yake kin jinin kasar Sin, ya bayyana cewa, a idon kasar Amurka, kasar Sin ba abokiyar gaba ba ce, amma tana kokarin hana kasar Sin da ta maye gurbin shugabancin duniya da yanzu kasar Amurka take zaune kan wannan matsayi. Wasu masu nazarin tattalin arziki sun taba yin hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2049, yawan GDP da kasar Sin za ta samu zai ninka sau uku bisa na kasar Amurka. Wannan ya zama wani misalin da Michael Pillsbury ya fi son yin amfani da shi a lokacin da ya ce, "a wannan yanayin da ake ciki, kasar Sin za ta sarrafa mu, kasarmu za ta zama yankin mulkin mallaka na kasar Sin."

Bisa wannan sabon kalamin da Michael Pillsbury ya yi, muna iya tabbatar da cewa, "cutar ana azabta mana" da Michael Pillsbury ya kamu da ita ta tsananta. A cikin littafinsa na "Gasar Marathon ta tsawon shekaru dari" da ya wallafa a shekarar 2015, ya taba bayyana cewa, wai kasar Sin na yin wani wasan dara da zai shafi shekaru dari domin kokarin wucewa kasar Amurka, wato ya zuwa shekarar 2049, wato a lokacin murnar cika shekaru dari na kafuwar Jamhuriyar Jama'a Sin, kasar Sin za ta maye gurbin kasar Amruka, za ta zama sabuwar kasaitacciyar kasa mai fada a ji a duk fadin duniya.

Kalaman da Michael Pillsbury ya yi a wannan karo na cewa, wai ba kawai kasar Sin za ta maye gurbin Amurka ba ne, har ma za ta yi mata mulkin mallaka. Gaskiya furucinsa abun dariya ne kuma ba shi da tushe balle makama.

Babu yadda za'a yi karya ta zama gaskiya. Burin da kasar Sin ke son cimmawa, buri ne na kowace kasa, wato samun 'yancin kai, da dunkulewar duk kasa gu daya, da kiyaye cikakken yankin kasa, jama'a kuma suna jin dadin zaman rayuwa, tattalin arzikin kasar ma zai bunkasa da kyau.

Tarihi na nuna cewa, kasar Sin ba ta taba yin babakere ko mulkin mallaka a sauran kasashe ba. Tun farkon karni na 15, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba shahararren mai kula da jiragen ruwan teku na kasar Sin Zheng He ya ziyarci kasashe da yankuna sama da talatin dake nahiyoyin Asiya da Afirka, inda ya kawowa mazauna wurare kayayyaki da nuna musu fatan alheri, da karfafa dankon zumunci tare da su. Bayan shekaru da dama, kasashen yammacin duniya sun fara zirga-zirga a jiragen ruwan teku, amma abun da suka kawowa mazauna wuraren su ne, kwace kaya da yin mulkin mallaka gami da cinikin bayi.

Ba kamar yadda ra'ayin da kasar Amurka take bi na yin takara a tsakanin kasa da kasa wadanda yawan ribar da suka samu ta yi daidai da yawan hasarar da sauran kasashe suka tabka ba, kasar Sin na tsayawa kan zaman daidai wa daida a yayin da take mu'ammala da kasashen ketare, wato ba ta yin la'akari da ko wadannan kasashe suna da girma ko kanana ne, ko suna da karfi ko ba su da karfi, ko kuma suna da arziki ko suna fama da talauci. A yayin da take kokarin inganta shawarar "Ziri daya da hanya daya", kasar Sin tana shan jaddada samun moriya tare ta hanyar hadin kai, tare kuma da bin manufar "yin shawarwari tare kan shirin hadin kai, da kafa dandalin hadin kai tare, da kuma more nasarorin da aka cimma sakamakon hadin kai". A kan batun tsaro kuma, tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekaru 70 da suka gabata, kasar ba ta taba tayar da yaki da rikici bisa radin kanta ba, a cikin shekaru kusan 40 da suka wuce, ta kwance damara sama da miliyan 4. A cikin takardar bayanin da a kwanan baya kasar ta bayar mai taken "Yadda tsaron kasar Sin yake a sabon zamani", an tabbatar da cewa, "ba za ta nemi matsayi don yin mulkin mallaka ba, ko neman fadada tasirinta kan wasu kasashen duniya, da yin babakere ga wasu kasashen duniya ba," wannan yana daga cikin muhimmin jigo na musamman game da ayyukan tsaron kasar Sin a sabon zamani. Akasin hakan, kasar Amurka na yin yaki a kusan kowace shekara, har ma yawan kasafin kudin sojanta a shekarar 2020 zai karu zuwa dala biliyan 750, wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar, kuma zai wuce jimillar yawan kudaden da kasashe 10 masu biye da ita ke kashewa a fannin.

A nata bangaren, kasar Sin na neman samun ci gaba ne da nufin kyautata zaman rayuwar jama'arta. Kuma bata da sha'awar maye gurbin wata kasa daban, kuma ba ta da ra'ayin zama 'yar sandar duniya. (Sanusi, Murtala, Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China