Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ghana za ta kasance cibiyar cinikayya cikin 'yanci a nahiyar Afirka a nan gaba
2019-07-26 14:09:44        cri

Yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka, wanda ya kasance yankin cinikayya cikin 'yanci da ya fi girma a duniya, ya soma aiki a farkon wannan wata, inda kuma kungiyar AU ta zabi birnin Accra, hedkwatar kasar Ghana a matsayin wurin da za a kafa sakatariyar yankin.

Game da hakan, malami mai koyarwa a jami'ar Ghana, kuma shehu malami a fannin tattalin arziki Adu Owusu Sarkodie, ya fitar da wani sharhi mai taken "Ghana na fatan cin gajiya sakamakon kasancewar wurin da za a kafa sakatariyar yankin cinikayya cikin 'yanci na Afirka", inda ya bayyana cewa, wannan kasa dake yammacin Afirka, za ta zama cibiyar cinikayya cikin 'yanci ta nahiyar Afirka a nan gaba.

A cikin sharhin, malam Sarkodie ya ce, Ghana ta ci nasarar zama kasa da za a kafa sakatariyar yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka, bayan ta shige gaban kasashen Masar, da Swaziland, Habasha, Kenya, Madagascar da kuma Senegal da dai sauransu.

Babban aikin na ofishin shi ne, gudanar da yarjejeniyar yankin cinikayya cikin 'yanci ta nahiyar Afirka. Ya zuwa yanzu, ban da kasar Eritea, kasashe guda 53 daga jimillar kasashe 54 na Afirka, sun sanya hannu kan yarjejeniyar, kana yarjejeniyar ta riga ta samu amincewa daga wajen hukumomin dokoki na kasashe guda 25. Yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka zai kasance wanda ya fi girma a duniya tun bayan kafuwar kungiyar WTO a shekarar 1995.

Sharhin ya kuma bayyana cewa, bisa tsarin yankin cinikayyar cikin 'yanci, kasashe mambobin sa sun amince da soke karbar haraji kan kayayyakin cinikayya da hidima, da kuma daina kayyade kayayyaki ko kafa katangar cinikayya a tsakaninsu. Bisa kididdigar da kwalejin Brookings ta kasar Amurka ta fitar, an cewa yawan cinikayya a tsakanin kasashen Afirka ya kai kashi 14 cikin dari bisa na jimilar cinikayyarsu gaba daya, amma adadin ya kai kashi 59 cikin dari a tsakanin kasashen Asiya. A tsakanin kasashen Turai kuma ya kai kashi 69 cikin dari.

Ya zuwa shekarar 2022, ana sa ran ganin yankin cinikayya cikin 'yanci na nahiyar Afirka ya taimaka wa babbar nahiyar, wajen samun karuwar cinikayyar da ake yi tsakanin kasashen nahiyar da kashi 52 cikin dari, wanda hakan zai shafi kasuwa mai yawan al'umma biliyan 1.2, kuma yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa zai kai dala triliyan 2.5.

Sharhin na ganin cewa, ayyukan sakatariyar za su hada da dauka da horar da ma'aikata, da aiwatar da manufofin da majalisar zartaswa ta tsara, da tuntubar manema labaru, da kuma shirya tarurruka, da tabbatar da asalin kudi, kana da yin bincike, da kimanta yadda ake gudanar da ayyuka bisa manufofi da shirye-shirye da aka tsara.

Wannan ne karo na farko da kasar Ghana ta karbi irin wannan aiki na zama sakatariya na wata kungiyar kasa da kasa. Sharhin ya bayyana fatansa na ganin kasar ta koyi fasahohin daga sauran kasashe suka samu.

Baya ga haka, Sarkodie ya bayyana a cikin sharin cewa, kasancewar wurin da za a kafa sakatariyar yankin cinikayya cikin 'yanci, zai sanya kasar Ghana ta kashe kudi, tare kuma da samun moriya ta hakan. Shugaban kasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya yi alkawarin samar da dala miliyan 10 don nuna goyon baya ga kafa sakatariyar. Ana kuma sa ran kungiyar AU ita ma za ta samar da kudi domin hakan.

A waje guda kuma, kasar Ghana na fatan ganin kafuwar sakatariyar, za ta taimake ta wajen ciyar da sana'ar hotel da sauran sana'o'in ba da hidima gaba, da kuma kara shahara a duniya. Ban da wannan kuma, karbar ma'aikata na sakatariyar ita ma za ta samar da guraban ayyukan yi masu yawa ga kasar.

A karshe dai, Sarkodie ya ce, har zuwa yanzu dai, ba a tabbatar da wa'adin karshe, na yaushe za a kafa sakariyar yankin cinikayya cikin 'yanci, da yaushe ne ofishin zai soma aiki ba. Kungiyar AU ita kanta ma na bukatar kawar da cikas a fannonin tsarin sakatariyar, da ka'idoji da tsare-tsare na ma'aikata, da kuma kasafin kudi.

Kasar Ghana tana arewacin bakin tekun gulf na Guniea dake yammacin nahiyar Afirka. Yammacin kasar na makwabtaka da kasar Cote d'Ivoire, yayin da arewacinta ke makwabtaka da kasar Burkina Faso, kuma gabashinta na makwabtaka da kasar Togo, kudancinta kuma na makwabtaka da tekun Atlantic. Fadin kasar ya kai muraba'in kilomita dubu 238.5, kuma yawan al'ummar kasar ya kai kimanin miliyan 29.5.

Bisa rahoton hasashen tattalin arzikin duniya, wanda kungiyar IMF ta bayar a watan Afrilun bana, an nuna cewa, yawan karuwar tattalin arziki na kasar ta Ghana zai kai kashi 8.8 cikin dari. Ana kuma sa ran za ta kasance kasa da za ta fi samun saurin karuwar tattalin arziki a duniya a shekarar 2019. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China