Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi shagulgulan tunawa da Nelson Mandela
2019-07-19 14:28:33        cri





A jiya Alhamis, an gudanar da jerin shagulgulan tunawa da ranar Nelson Mandela a hedkwatar MDD da ke New York. Babban sakataren MDD Antonio Gutterres da ma shugabar babban taron MDD María Fernanda Espinosa sun bayyana cewa, akidar Nelson Mandela na da muhimmiyar ma'ana ta fuskar kiyaye zaman lafiya da jituwa a duniya.

A jiya Alhamis, an gudanar da taron tunawa da ranar Nelson Mandela ta kasa da kasa a hedkwatar MDD da ke birnin New York na kasar Amurka, inda babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi kira da a ci gaba da kokarin yada akidar Nelson Mandela, tare da kare tsarin dokokin MDD. Ya ce, "Yau muna tunawa da gudummawar da Nelson Mandela ya bayar ga Afirka ta Kudu da ma duniya baki daya a tsawon rayuwarsa, muna kuma jinjina masa a matsayin daya daga cikin jagororinmu da suka kasance alamar zamaninmu tare da ba mu kwarin gwiwa. Nelson Mandela alama ce ta jaruntaka da tausayi, haka kuma misali ne na kokarin da ake yi wajen kiyaye 'yanci, da zaman lafiya, da kuma adalci. Ya tsaya tsayin daka a kan wadannan ka'idoji, kuma a shirye yake a kullum ya sadaukar da ransa."

A ranar 24 ga watan Satumban bara, MDD ta gudanar da taron kolin Nelson Mandela kan zaman lafiya a hedkwatarta da ke New York, kuma a wancan rana, kasashe mahalarta taron sun gabatar da wata sanarwa, inda suka yi alkawarin daukar matakai na raya al'umma mai zaman lafiya, da adalci, da hakuri da juna ba tare da nuna bambanci ba. Sanarwar ta ce, kabilanci, da nuna bambancin al'ummomi, da nuna kyamar baki sun saba wa manufar MDD, a yayin da martaba kasancewar al'adu da kabilu da ma addinai iri daban daban ke da matukar muhimmanci wajen cimma dauwamammen zaman lafiya, da sulhu, da kuma karfafa zumunci a tsakanin al'ummomi daban daban. Taron ya kuma sanar da mai da shekarar 2019 zuwa 2028 a matsayin shekaru 10 na zaman lafiya na Nelson Mandela.

A yayin taron da aka gudanar a jiya, Mr.Antonio Guterres ya bayyana cewa, shekarar 2019 ita ce shekara ta farko daga cikin shekaru 10 na zaman lafiya na Nelson Mandela, amma har yanzu, ana fama da rikice-rikice a wasu sassan duniya ba tare da gano alamar kawo karshensu ba, don haka, a daidai wannan lokaci, kiran da Nelson Mandela ya yi na kiyaye zaman lafiyar duniya na da matukar muhimmanci. "A halin da ake ciki yanzu, kalaman nuna kiyayya na kara haifar da illa ga sassan duniya. Don haka, kiran da Nelson Mandela ya yi na karfafa hadin kan al'umma da zaman lafiya na da ma'ana ta musamman. A watan da ya wuce, na ayyana shirin yaki da kalaman nuna kiyayya, don daidaita ayyukan da MDD ke yi na bincike tare da rigakafin irin wadannan kalaman."

A shagulgulan da aka gudanar, shugabar babban taron MDD María Fernanda Espinosa tare da sauran jami'an diplomasiyya na MDD sun kai ziyarar musamman Brownsville da ke unguwar Brooklyn, inda suka dafa abinci ga al'ummar wurin tare da gudanar da ayyukan sa kai. Rahotanni na cewa, Nelson Mandela ya taba zuwa unguwar a lokacin da ya fara zuwa New York a shekarar 1990.

A wannan rana, Madam María Fernanda Espinosa ta bayyana fatanta cewa, za a martaba akidar Nelson Mandela, ta yadda za a yi nasarar kawar da sabani tare da hada kan juna, don tinkarar tsoffi da sabbin kalubalolin da ake fuskanta. Ta ce, "Ya kamata mu martaba akidar Nelson Mandela fiye da kowane lokaci a baya, ya kamata mu yi shawarwari da juna da kuma sauraron ra'ayoyin juna, musamman ma ya kamata mu mai da hankali a kan al'ummomin da a kan yi fatali da su. Ya kamata mu kara amincewa da hadin gwiwa da juna, kuma mu dauki nauyin da ke bisa wuyanmu, ta yadda za mu iya tinkarar matsalolin da muke fuskanta, ciki har da matsalar sauyin yanayi, da rikici, da nuna karfin tuwo, da talauci, da rashin adalci. Hanyar da ta fi dacewa wajen daukaka Nelson Mandela ita ce kiyaye duniyarmu ta bai daya. "

An haifi Nelson Mandela a ranar 18 ga watan Yulin shekarar 1918 cikin wani iyali na sarauta a kasar Afirka ta Kudu, kuma ya dukufa a kan tabbatar da zaman daidaito a tsakanin al'ummomi daban daban. Ya taba shafe tsawon shekaru 27 a gidan kurkuku. A kokarin da ya yi, an kai ga kawar da wariyar launin fata a kasar ta Afirka ta Kudu kuma cikin lumana. A watan Mayun shekarar 1994, Nelson Mandela ya zama shugaba bakar fata na farko a Afirka ta Kudu. Ya riga mu gidan gaskiya a ranar 5 ga watan Disamban shekarar 2013,

A watan Nuwamban shekarar 2009, babban taron MDD ya zartas da kuduri, inda aka yanke shawarar ware ranar 18 ga watan Yulin kowace shekara a matsayin ranar Nelson Mandela.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China