Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace a kara mai da hankali kan hakkin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki yayin kwaskwarimar IMF
2019-07-17 19:44:13        cri

Jiya Talata hukumar zartaswar asusun ba da lamuni na kasashen duniya ko IMF a takaice, ta sanar da cewa, ta amince da rokon murabus da shugabar asusun Christine Lagarde ta gabatar, kuma za ta fara aikin zabar sabon shugaban asusun nan take.

Yanzu haka ana gudanar da bincike karo na 15 kan aikin asusun, a don haka ya kamata a zabi wani wanda zai yi kokari kan aikin kwaskwarimar asusun, domin biyan bukatun zamanin da ake ciki, haka kuma ya dace a kara mai da hankali kan hakkin nuna ra'ayi, da wakilci na kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki, da kasashe masu tasowa yayin da ake gudanar da gyaran fuska kan tsarin asusun IMF, ta yadda za a gudanar da aikin asusun bisa doka.

Bisa matsayinsa na sashe daya daga cikin tsarin Bretton Woods, wanda ke karkashin jagorancin kasashen Amurka da Turai, asusun IMF yana nuna kwazo da himma kan aikin hadin gwiwar kudaden kasa da kasa, da samar da jari da tallafi, da kiyaye daidaiton kudin kasa da kasa, musamman ma tun bayan shekarar 2000, tsarin tattalin arzikin duniya ya samu manyan sauye-sauye, wato wasu kasashe sun samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri, har ta kai suna taka babbar rawa a cikin harkokin tattalin arzikin duniya, tare kuma da ba da karin gudummowa ga ci gabansa.

A wani bangaren kuma, tsarin gudanar da harkokin tattalin arzikin duniya na yanzu ba ya ba da amfani sosai a fannonin sassauta rashin daidaiton tattalin arzikin duniya, sa kaimi ga cinikayya tsakanin bangarori da dama, da ma warware matsalar basussukan da wasu kasashe suka fuskanta. Sabo da haka, yadda za a sa kaimi ga aikin gyare-gyare na IMF, da kyautata ikon fada a ji na kasashe masu saurin ci gaba, da masu tasowa a cikin harkokin tattalin arzikin duniya ya dace da ci gaban zamanin yanzu.

Amma, idan muka duba matsayin kasashe a cikin tsarin tattalin arzikin duniya, to za a iya gano cewa, kasonsu cikin IMF da ma yadda ake tafiyar da harkokin asusun ba ya bayyana canjin tsarin.

Alal misali, jimillar GDP da kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa ke samarwa, ya zarce kaso 50 bisa na duk duniya. Yawan gudummawar da suke bayarwa ga karuwar tattalin arzikin duniya ma ya zarce kaso 80, yayin da tattalin arzikin Amurka ya ragu zuwa kimanin kaso 20 kawai. Amma har yanzu Amurka na da ikon jefa kuri'a mafi girma a cikin IMF, wanda ya kai kaso 16.52. A kan muhimman kudurorin asusun kuwa, Amurka na da ikon kin amincewa, kasashe masu sukuni kuma na da rinjayayyen matsayi.

Yanayin yawan kuri'un da kasa da kasa suka iya jefa bai yi daidai da matsayinsu a duniya ba, wato zai kawo illa ga samun moriyar sabbin kasashe mafiya samun ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa, tare da wakilci da adalci na asusun IMF. Don haka, mukaddashin shugaban asusun IMF na yanzu David Lipton, ya yi kira da tabbatar da mutuncin asusun IMF da albarkatunsa, kuma tilas ne a daga ikon yin magana na kasashe mafiya samun ci gaban tattalin arziki, tare da daukar alhakinsu yadda ya kamata.

A halin yanzu, an yi bincike kan yawan kaso da kasa da kasa ke samu a cikin asusun IMF karo na 15, kuma watakila za a cimma daidaito kan sabon tsari a wannan fanni, da sake daidaita yawansu bisa tsarin. Ta hakan, asusun IMF zai iya tabbatar da tsarinsa cikin adalci bisa dokoki, kuma zai iya tinkarar rikice-rikice, da tabbatar da hada-hadar kudi a duniya, da kuma sarrafa tattalin arzikin duniya cikin adalci yadda ya kamata. (Masu Fassarawa: Jamila, kandeļ¼ŒZainab daga CRI Hausa)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China