Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD: Tsarin hada-hadar kudi na zamani zai taimakawa Afirka cimma nasarar SDGs
2019-07-16 10:17:44        cri
Darektan sakatariyar kwamitin da babban sakataren MDD ya kafa kan tsarin hada-hadar kudi na zamani game da manufofin ci gaba mai dorewa(SDGs) Tillman Bruett, ya bayyana cewa, fasahohi game da harkokin kudi, za su karfafawa dukkan bangarorin al'ummar nahiyar Afirka cin gajiyar hidimomin kudi.

Jami'in ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin Kenya cewa, tsarin harkokin kudi na zamani, ya samarwa magidanta wata dama ta daukar nauyin manufofin samun ci gaba mai dorewa da kansu, ta hanyar samar musu da tsarin kiwon lafiya, da makamashi mai tsafta inda za su rika biyan kudin wutar lantarki da suka yi amfani da shi.

Tillman ya bayyana hakan ne, a gefen taron kaddamar da tsarin hada-hadar kudi na zamani tsakanin Afirka da Asiya mai suna Afro-Asia FinTech..

Taron na kwanaki biyu, ya samu halartar sama da masu tsara manufofi da shugabannin masana'antu 1,500 daga sama da kasashen Afirka da Asiya 45, inda ake sa ran za su karfafa amfani da tsarin na Fintech a shiyyoyin biyu.

A cewar jami'in na MDD, tsarin amfani da hada-hadar kudi na zamani na kara samun karbuwa a Afirka, musamman kasashen Kenya da Uganda da Tanzaniya da kuma Zimbabwe.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China