Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Aljeriya ta kai wasan karshe a gasar AFCON bayan doke Najeriya
2019-07-15 09:55:30        cri

Dan wasan Manchester City Riyad Mahrez ya yi nasarar jefa kwallo a bugun tazara a minti na karshe na wasan kusa da na karshe na gasar AFCON da Aljeriya ta bugu da Najeriya a daren ranar Lahadi, inda ta doke Najeriya da ci biyu da 1. Matakin da ya baiwa Aljeriyar damar kaiwa ga wasan karshe na gasar.

Mahrez wanda aka bayyana a matsayin gwarzon dan wasa, ya ce, Najeriya ba kwanwar lasa ba ce. A nasa tsokacin mai horas da 'yan wasan Aljeriya Djamel Belmadi, ya ce, ya san cewa, wasan zai yi zafi, saboda karfin tawagar Najeriyar da ma yadda 'yan wasan na Aljeriya suka gaji.

Najeriya ta yi nasarar jefa kwallonta ne a mituna 71 na wasan, a bugun daga kai sai mai tsaron gida ta hannun dan wasan gabanta Odion Ighalo dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua dake kasar Sin, bayan da na'urar dake taimakawa alkalin wasa ta tabbatar da cewa, dan wasan Aljeriya ya taba kwallon da hannu.

Mai horas da 'yan wasan Najeriya Gernot Rohr, ya amince cewa, 'yan wasan gaba Aljeriya sun matsawa masu tsaron bayan Najeriya lamba, abin da ya sa suka rude.

A ranar 21 ga watan Yuni ne dai aka bude gasar cin kofin kwallon kafan Afirka na 32 a kasar Masar. Za kuma a kammala gasar ce a ranar Jumma'a 19 ga watan na Yulin, inda za a buga wasan karshe tsakanin Aljeriya wadda ta lashe kofin gasar a shekarar 1990 da kasar Senegal wadda ta doke kasar Tunisa da ci 1 da nema a daya wasan kusa da na karshen da aka buga. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China