Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta sanyawa kamfanonin Amurka dake sayarwa yankin Taiwan makamai takunkumi
2019-07-13 21:34:57        cri

Amurka ta amince da sayar da wasu makaman da darajarsu ta zarce dala biliyan 2.2 ga yankin Taiwan na kasar Sin a kwanakin baya. Game da hakan, ma'aikatar harkokin wajen Sin ta sanar jiya cewa, kasar za ta garkamawa kamfanonin Amurka wadanda suka sayarwa Taiwan makamai takunkumi, al'amarin da ya zama wani babban matakin da ya wajaba da kasar Sin ta dauka don kare babbar moriyarta.

Kowa ya sani, Taiwan wani yanki ne da ba za'a iya balle shi daga kasar Sin ba. Sayarwa Taiwan makamai da Amurka ta yi, ba keta dokoki gami da ka'idojin kasa da kasa kadai ya yi ba, har ma da sabawa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya gami da wasu sanarwa uku da Sin da Amurka suka daddale cikin hadin-gwiwa. Sayarwa yankin Taiwan makamai da kamfanonin Amurka suka yi, ba ciniki ne kawai suka yi ba, aika-aika ce da ta lahanta ikon mallakar kasar Sin da hakkin tsaron kasar. Don haka, takunkumin da kasar Sin ta sanyawa kamfanonin Amurka ya dace da halin da ake ciki kuma bisa doka, kana, gwamnatin kasar Sin gami da kamfanoninta ba za su yi duk wani hadin-gwiwa ko ciniki tare da kamfanonin kasashen waje wadanda suka illata moriyar kasar ba.

Shekaru 40 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Amurka, kasar Amurka ta bayyana cewa, za ta bi hadaddiyar sanarwa guda uku da kasashen biyu suka cimma, kuma ta amince da kasancewar Sin daya tak a duniya, Taiwan wani sashe ne na kasar Sin, kana kuma gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin halaltacciyar gwamnati ce daya kacal ta kasar ta Sin, bayan haka kuma ta yi alkawarin takaita sayarwa Taiwan makamai a hankali har zuwa lokacin da aka warware matsalar. Amma, a sa'i daya kuma ta yi amfani da dokarta game da akalar dake tsakaninta da Taiwan, don ci gaba da mu'amala da mahukuntan Taiwan, da yin cudanya a fannin soja, da nufin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin. A 'yan kwanakin baya kuma, majalisar dattawa da majalisar wakilan kasar Amurka sun zartas da shirin dokar mika iko game da kasafin kudi na tsaron kasa na shekarar 2020 daya bayan daya, don ci gaba da goyon bayan sayar da makamai ga Taiwan.

Ko Amurka ta dauki matakin sayarwa Taiwan makamai, da nufin tabbatar da tsaron Taiwan? Ko shaka babu, ba haka ba ne, saboda a kasar Amurka, a bayyane yake cewa gwamnati na da alaka mai karfi da kamfanonin kera makamai. Amma, sayarwa Taiwan makamai da kamfanonin kasar Amurka ke yi ba wani mataki ne na neman riba ba, ya zama wani mataki na lalata mulkin kan kasar Sin da kutsa kai cikin harkokin kasar. Don haka, kasar Sin ba za ta yi hakuri a kai ba. Bayan shekaru hudu kasar Sin ta kara saka takunkumi kan kamfanonin Amurka masu shiga aikin sayarwa Taiwan makamai, wannan ya nuna cewa, kasar Sin ba za ta janye jiki kan batun dake shafar kiyaye mulkin kan kasa ba, da kuma niyyarta wajen kiyaye mulki da cikakken yankin kasa.(Murtala Zhang, Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China