Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron kolin kasashen Afrika ya cimma matsayar daukar matakan yaki da ta'addanci
2019-07-12 10:50:11        cri
Babban taron shiyyar Afrika wanda aka kammala a jiya Alhamis game da yaki da ta'addanci an zartar da kudurorin daukar matakan yaki da barazanar ta'addanci wanda ke matukar dakile cigaban tattalin arziki da wargaza zaman lafiyar nahiyar Afrika.

Wakilai 1,500 daga kasashen mambobin kungiyar tarayyar Afrika AU, da kungiyoyin gamayyar kasa da kasa, da kungiyoyin fararen hula, da masana daga cibiyoyin ilmi ne suka halarci taron kolin, wanda aka gudanar tsakanin 10-11 ga watan Yuli, inda aka tattauna sabbin dabarun yaki da ayyukan ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini a nahiyar ta biyu mafi girma a duniya.

Fred Matiang'i, sakataren ma'aikatar harkokin cikin gidan Kenya, a cikin jawabinsa na rufe taron, ya bukaci kasashen Afrika su hada kai don yin aiki tare da nufin kakkabe ayyukan ta'addabci daga tushe, tare da zakulo masu tallafawa ayyukan ta'addanci da masu samar musu da kudade.

"Ya zama tilas mu kara zage damtse wajen kawar da dukkan wani tunanin dake tabbatar da yada manufofin ta'addanci, tare da neman mafita wajen kawar da duk wasu kalamai dake haifar da kiyayya da rarraba kan jama'a," inji Matiang'i. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China