Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kafa yankin ciniki maras shinge a Afirka a hukumance
2019-07-09 11:20:07        cri

Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, ta bude taron koli na musamman karo na 12 kan yankin ciniki maras shinge na Afirka a ranar 7 ga wata a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar, inda aka sanar da kafa yankin a hukumance.

A yayin bikin bude taron kolin na AU, shugaban kwamitin kula da harkokin kungiyar Moussa Faki Mahamat ya gabatar da jawabi, inda ya sanar da cewa, kasashen Najeriya da Benin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa yankin ciniki maras shingen Afirka ta AfCFTA, kuma sun mika takardun amince da yarjejeniyar. Sabo da haka, ya zuwa yanzu, ban da kasar Eritrea, kasashe 54 cikin mambobin kungiyar AU 55 sun riga sun daddale yarjejeniyar, baya ga yadda mambobin 27 suka mika takardun amincewa da yarjejeniyar ga kwamitin kungiyar, bayan da suka samu amincewa bisa dokokin kasashensu.

Hakika dai, yarjejeniyar AfCFTA ta fara aiki ne a ranar 30 ga watan Mayu na bana. Idan dukkan kasashe mambobin kungiyar 55 suka daddale ta, inda yankin ciniki maras shinge na Afirka zai zama irin yankin mafi girma a duk duniya, bisa la'akari da yawan mambobinsa. Kuma ana sa ran za a samu wata babbar kasuwa da ta shafi mutane biliyan 1.2, kuma jimillar GDPn ta zai kai dala triliyan 2.5.

Stephen Karingi, kwararre a kwamitin kula da tattalin arzikin Afirka na MDD ya bayyana cewa, yankin zai taimaka wajen rage katangar kudin haraji, lamarin da zai samar da sauki ga shige da ficen kayayyaki cikin nahiyar Afirka da ma zuwa ketare, baya ga kyautata muhallin zuba jari na duk nahiyar.

Ban da wannan kuma, Mr. Karingi ya ce, kafuwar yankin ciniki maras shinge na Afirka, zai samar da damammaki ga hadin kan Sin da Afirka. A cewarsa, idan aka dauki sana'ar sararin samaniya a matsayin misali, to za a gano cewa, ko da yaushe Sin na rike da fasahohin zamani a wannan fannin, ana sa ran Sin za ta taimakawa kasashen Afirka daban daban wajen kawar da yadda suke dogaro da fasahohin sararin samaniya na kasashen yammacin duniya, bisa manufofin yankin da abin ya shafa.

A nasa bangaren kuma, shugaban cibiyar nazarin harkokin kasar Sin na Najeriya Charles Onunaiju ya furta cewa, kafuwar yankin ciniki maras shinge, ta zama tamkar wata ishara ce a yunkurin dunkulewar Afirka gu daya. Bayan da aka fara aiwatar da yarjejeniyar, sannu a hankali za a rage shingayen cinikayya cikin nahiyar, kuma za a kyautata muhimman ababen sadarwa, da habaka cinikayya tsakanin kasashen Afirka, da sa kaimi ga kyautata tsarin masana'antun kasashen, da ma gaggauta yunkurin raya masana'antu a nahiyar.

Amma a waje daya kuma, Onunaiju ya nuna cewa, sakamakon karancin kyawawan muhimman ababen more rayuwa, da rashin daidaiton ci gaba, akwai sauran rina a kaba, ganin yadda kasuwar gu daya ta Afirka ta sa kaimi ga tattalin arzikinta. Nahiyar Afirka na bukatar kasar Sin da sauransu, su goyi bayan yunkurinta na samun dunkulewa. Shirin hadin kan Sin da Afirka wajen raya masana'antu da shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ke kokari a kai a 'yan shekarun nan, sun dace da burin ci gaban Afirka. Afirka na sa ran ganin Sin ta ci gaba da taimaka mata wajen raya muhimman ababen more rayuwa, da ma kyautata matsayinta na sadarwa da cudanya da juna.

Haka zalika ma, Onunaiju ya ce, Sin cibiyar duniya ce a fannin masana'antu, wadda sha'anin kudi da na kasuwanci a Intanat nata ke samun babban ci gaba. Kafuwar yankin ciniki maras shinge na Afirka, zai inganta hadin kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin Afirka da Sin. Sin na iya raya wasu masana'antu a Afrika, wanda hakan zai taimaka wa nahiyar wajen kara darajarta a duniya.

Farfesa Walid, masani a fannin ilmin tattalin arziki na Jami'ar Cairo yana ganin cewa, dimbin kamfanonin Sin da Sinawa masu zuba jari, za su ci gajiya yayin da ake kokarin raya yankin ciniki maras shinge na Afirka. Kuma ya ce, kyawawan manufofin da ke da nasaba da yankin, za su zama muhimman matakan Masar wajen jawo jarin kasar Sin. Bugu da kari, kasashe daban daban na Afirka, za su kara cudanya da juna a fannin ciniki sakamakon kafuwar yankin, lamarin da zai samar da sauki ga Sin wajen raya ayyukanta a Afirka cikin dogon lokaci.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China