Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkaluman nazarin tattalin arziki na kungiyar OECD ya nuna daidaituwar karfin ci gaban tattalin arziki
2019-07-09 10:49:55        cri

Alkaluman nazarin tattalin arziki (CLIs) na kungiyar kawancen kasashe domin raya tattalin arziki da samar da ci gaba OECD da aka wallafa a jiya, sun nuna cewa, karfin ci gaban tattalin arzikin kasashen kungiyar na daidaituwa.

Kungiyar ta ce alkaluman sun nuna daidaituwar karfin ci gaba a tsakanin kasashenta, biyo bayan saukin da ya yi a nazarin da aka yi watan da ya gabata.

Kusan alkaluman ba su sauya ba a kan maki 99 tsakanin kasashen, yayin da suka nuna cewa, karfin ci gaban kasashe 7 mafiya karfin tattalin arziki, ya yi sauki.

Alkaluman na sa ran karfin tattalin arzikin Amurka zai yi sauki, yayin da na bangaren masana'antun kasar Sin zai daidaita.

Alkaluman na da nufin samar da alamun sauyi tun da wuri, kamar na karuwar ko raguwa tsakanin fadadar tattalin arziki da akasinsa, watanni 6 kafin lokacin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China