Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalilai Ukun Da Suka Sa Duniya Ta Kara Dogara Kan Tattalin Arzikin Sin
2019-07-08 20:30:27        cri

 

Cibiyar nazarin harkokin duniya ta McKinsey Global Institute ta fitar da wani rahoto a kwanakin baya, inda ya ce, daga shekara ta 2000 zuwa 2017, kaso 0.4 zuwa na 1.2 na duniya na kara dogara kan tattalin arzikin kasar Sin. Hakan na nuna cewa, yayin da Sin ke kara shiga harkokin kasa da kasa, tana kuma dada bada gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, har ma kasashen duniya na kara nuna yakini ga tattalin arzikinta.

Bankin duniya ya yi hasashen cewa, daga shekarar 2012 zuwa 2016, yawan gudummawar da Sin ta bayar ga habakar tattalin arzikin duniya ya kai kaso 34 bisa dari, adadin da ya zarce jimillar yawan gudummawar da Amurka da tarayyar Turai gami da Japan suka bayar. Kasashen duniya na kara dogara ne kan tattalin arzikin kasar Sin duba da irin babbar gudummawar da take bayarwa ga ci gaban harkokin duniya.

Da farko, kasar Sin tana da babbar kasuwa da rukunin matsakaita masu kudin shiga a duniya, wannan ya sa ake samun karuwar masu sayayya, hakan ya kuma taimaka wajen ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Cibiyar nazarin harkokin duniya ta McKinsey ta ruwaito kididdigar bankin duniya na cewa, daga shekarar 2010 zuwa 2017 kasar Sin ta ba da gudummowar kashi 31 cikin dari na duk duniya a fannin karuwar iyalai masu sayayya, kuma kasar ta kasance babbar kasuwa ta farko a duniya a fannonin motoci, barasa, wayoyin salula da dai sauransu. A wani bangaren, kasar Sin ta shigo da kayayyaki masu yawa, hakan ya taimaka wa sauran kasashe wajen samun bunkasuwar tattalin arziki. Bisa kididdigar da aka fitar, daga shekarar 2001 zuwa 2017, matsakaicin karuwar jimillar cinikayyar shigo da kayayyaki na kasar Sin ya kai kashi 13.5 cikin dari, wanda ya karu da kashi 6.9 cikin dari bisa na duk duniya. A dayan bangaren kuma, babbar kasuwar kasar Sin ta samar da dama mai kyau ga kamfanonin kasashen ketare dake kasar. A shekarar 2017, kamfanonin kasashen ketare sun samar da gudummowar kusan kashi 50 cikin dari bisa na cinikayyar waje na kasar Sin, da kuma babbar riba ta kashi 1 cikin 4 a fannin masana'antu, duk da cewa, adadinsu kashi kusan 3 ne cikin dari kawai bisa na kamfanonin kasar ta Sin. Hukumomi da dama sun yi hasashen cewa, mai yiwuwa ne ya zuwa shekarar 2030 karuwar masu sayayya za ta kai dala triliyan 6, makamantan jimillar kudin inda aka hada Amurka da yammacin Turai, wanda zai kara inganta hada kan duniya da Sin a fannin tattalin arziki.

Har wa yau, kasar Sin ita ce kasa daya kacal a duniya da take da dukkannin nau'o'in masana'antu, abin da ya ba ta kwarewa ta fannin samar da kayayyaki. Cibiyar nazari ta McKinsey ta bayar da rahoton cewa, kusan dukkanin sana'o'in duniya na dogara ga kasar Sin a wani bangare, inda daga cikin sana'o'i 20 da aka yi nazari a kansu, sana'o'i 17 na kasar Sin ne.

Ya kamata a lura da cewa, jarin da kasar Sin take zubawa a kasashen ketare shi ma na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da karuwar tattalin arzikin duniya. A matsayinta na kasa ta biyu a duniya wajen zuba jari a sauran kasashen duniya, a shekarar 2018, yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasashen ketare ya kai dalar Amurka biliyan 130, ta kuma samar da guraben aiki miliyan 17 a kasashen da ta zuba jarin. Ma iya cewa, jarin da kasar Sin ta zuba ya samar da riba ga irin wadannan kasashe, matakin da tabbas zai karfafa huldar tattalin arziki a tsakanin Sin da kasashen.

A yayin da tsarin ba da kariyar ciniki da kuma ra'ayi na kashin kai suke ta kawo illa ga tsarin masana'antun duniya da kasuwar hada-hadar kudi, kasar Sin ta kuma kara daukar matakai na zurfafa gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, matakan da za su tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wanda kuma ke da matukar muhimmanci. (Murtala Zhang, Bilkisu Xin, Lubabatu Lei)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China